Shehu Sani ya lissafo dalilai 3 da yasa manyan Arewa su kayi gum a kan yawaitar kashe-kashe a yankin

Shehu Sani ya lissafo dalilai 3 da yasa manyan Arewa su kayi gum a kan yawaitar kashe-kashe a yankin

Sanata Shehu Sani mai wakiltan Kaduna ta tsakiya a majalisar dattawa ya zargi 'yan bokon arewa da yin gun da bakinsu a kan kashe-kashen da ake yi a yankin na arewa.

Dan majalisar ya yi wannan zargin ne ta shafinsa na sada zumunta na Twitter a yau Litinin.

Ya kuma lissafo dalilai uku da ya ke ganin sun saka 'yan bokon na arewa shiru a kan kashe-kashen kamar haka:

Shehu Sani ya zargi 'yan bokon arewa da yin gum a kan kashe-kashe

Shehu Sani ya zargi 'yan bokon arewa da yin gum a kan kashe-kashe
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Karin aure da manoma keyi ya janyo hayayafar al'umma a Najeriya - Minista

1. Akwai yiwuwar suna tsoron a rika yi musu kallon masu adawa da gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari.

2. Wasu daga cikinsu na ganin shugaba Muhammadu Buhari yana iyaka kokarinsa sai kuma na uku

3. Zai yiwu ba su damu da halin da talakawa da al'ummar arewan suke ciki bane kwata-kwata domin kashe-kashen bai cika shafen su ba.

Kalamansa, "Manyan 'yan bokon arewa suna shiru ne game da kashe-kashen da akeyi a arewa saboda dalilai gudu uku; Tsoron a rika yi musu kallon masu adaawa da gwamnati; Wasu sunyi imanin shuagaban kasa yana iya kokarinsa; Halin ko in kula saboda talakawa ne ke mutuwa."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel