Tarin bashi yana cikin abin da ya sa ake fama da karancin lantarki

Tarin bashi yana cikin abin da ya sa ake fama da karancin lantarki

Sanin kowa ne cewa har yanzu ana fama da rashin wuta a cikin Najeriya duk da kokarin da gwanatin kasar ke yi. Jaridar Reuter tayi nazari game da abin da ya hana a samu isasshen wuta a kasar.

Tarin bashi yana cikin abin da ya sa ake fama da karancin lantarki

Ministar harkokin wutan lantarki na Najeriya Babatunde Fashola
Source: Depositphotos

Daga cikin dalilan da ya sa ake wahalar wuta a kasar akwai rashin kudi. Yanzu haka, Kamfanin NBET ne yake da alhalin sayen karfinwuta sannan ya rabawa ‘yan kasuwa, wanda su kuma su ke kai wutar lantarkinzuwa gida-gida.

Sai dai irin su Hukumar NBTE su na fama da karancin kudi domin ‘yan kasuwan ba su biyan Gwamnati kudin da su ka kashe wajen sayen karfin wutan. Wannan ya sa manyan tashoshin wutan lantarki su ke fuskantar babban kalubale.

Duk ana fama da wannan matsaloli a kasar ne saboda rashin biyan kudin wuta a wajen jama’a. Ko da kamfanonin da ke raba wutan sun saki lantarki, kudin su ba ya fitowa a hannun jama’a, don hake su ma su ke fama da asara iri-iri.

KU KARANTA: Ba zan sake sa hannu a kan wani kudiri a yanzu ba – Buhari

Irin wadannan matsaloli ne ya sa tarin bashi yayi wa kamfanonin wutan katutu a Najeriya. Yanzu haka dai babban bankin duniya na shirin ba Najeriya bashin Dala biliyan 1 domin ganin an kawo gyara a sha’anin wutar lantarkin kasar.

Har yanzu mafi yawan mutane ba su da na’urar da ke auna wutan lantarkin da aka sha, wannan ya sa kamfanonin ke aiki da molar-ka wajen karbar kudin wuta daga hannun mutane. Hakan ya sa kamfanonin su ke tashi babu ribar kirki.

A 2013 ne tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya saidawa ‘yan kasuwa kamfanin wutan lantarki na kasar. Yanzu dai akwai bashin da ya haura Tiriliyan 1.3 a kan wuyan kamfanonin inji jaridar Reuters.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel