Ka fada mana abin da kayi lokacin ka na Gwamna-Okorocha ya fadawa Oshiomhole

Ka fada mana abin da kayi lokacin ka na Gwamna-Okorocha ya fadawa Oshiomhole

- Rochas Okorocha ya kalubalanci shugaban APC ya fadi aiki da yayi a Jihar Edo

- Gwamnan na Jihar ya jefawa shugaban jam’iyyar APC wannan kalubale ne jiya

- Okorocha yace bai zai fa kyale Oshiomhole ya zo har Jihar sa ya ci masa fuska ba

Ka fada mana abin da kayi lokacin ka na Gwamna-Okorocha ya fadawa Oshiomhole

Rikicin Rochas Okorocha da Shugaban APC Oshiomhole yayi kamari
Source: Getty Images

Mun samu labari cewa Gwamnan Jihar Imo, Rochas Okorocha, yayi kaca-kaca da shugaban APC na kasa watau Adams Oshiomhole bayan tsohon Gwamnan ya shiga Jihar Imo ya taya ‘Dan takarar APC yakin neman zaben 2019.

Rochas Okorocha, wanda yake shirin barin karagar mulki, ya maidawa Adams Oshiomhole martani bayan ya fito ya bayyana cewa za su maka wasu Gwamnoni da ‘Yan takara kara a gaban hukumar zabe na kasa watau INEC.

Okorocha yayi watsi da barazanar shugaban jam’iyyar ta APC inda yace surutanbanza kurum yake yi. Okorochahar ta kai ya nemi Oshiomhole ya fito ya lissafa ayyukan da yayi a lokacin yana gwamna a Jihar Edo har na wa’adi 2.

KU KARANTA: Abin da Buhari ya fadawa Shugaban Darikar Qadriyya a game da zaben 2019

Shugaban gwamnonin na APC yace Oshiomhole ya bar mulki, ma’aikata su na bin sa bashin albashi na watanni. Gwamnan yace shugaban na APC ya daina kokarin ci masa mutunci a Imo, ya tsaya yayi wa ‘Dan takaran sa kamfen.

Oshiomhole ya caccaki wasu gwamnoni da yace ba su biyan albashi. Wannan yasa Gwamnan ya maida martani ta bakin babban Sakataren sa, Sam Onwuemeodo inda ya nemi tsohon gwamnan ya lissafo aikin da yayi wa Jihar Edo.

Rochas Okorocha.da Ibekunle Amosun su na ta samun sa-in-sa da APC game da ‘Dan takarar gwamna a Jihohin su. A Imo dai, APC ta tsaida Hope Uzodinma ne, inda shi kuma Gwamna Okorocha yake bayan Uche Nwosu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Mailfire view pixel