Shugaba Buhari yayi Allah wadai da kashe-kashe a Zamfara

Shugaba Buhari yayi Allah wadai da kashe-kashe a Zamfara

- Shugaba Buhari yayi watsi da kashe-kashe a garin Birnin Magaji da ke karamar hukumar Tsafe da kuma garin Magami da ke yankin Faru na karamar hukumar Maradun

- Buhari ya bayyana kashe-kashen a matsayin wanda ya munana

- A baya-bayan nan dai jihar Zamfara na fama da yawan hare-hare daga yan fashi

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari yayi Allah wadai da kashe-kashe a garin Birnin Magaji da ke karamar hukumar Tsafe da kuma garin Magami da ke yankin Faru na karamar hukumar Maradun da ke jihar Zamfara.

A wani jawabi daga Garba Shehu wanda ya kasance babban mai ba shugaban kasa shawara a kafofin watsa labarai a ranar Litinin, 24 ga watan Disamba, Buhari ya bayyana kashe-kashen a matsayin wanda ya munana.

Shugaba Buhari yayi Allah wadai da kashe-kashe a Zamfara

Shugaba Buhari yayi Allah wadai da kashe-kashe a Zamfara
Source: Depositphotos

Shugaban kasar ya umurci shugaban hafsan sojin sama, Marshall Abubakar Baba Sadiq da ya kai wani ziyarar gani da ido a Zamfara da Sokoto.

KU KARANTA KUMA: Dan takarar shugaban kasa a APC ya sauya sheka zuwa PDP

An kuma tattaro cewa shugaban kasar na duba yiwuwar amfani da ayyukan sojoji domin kawo karshen rikicin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel