Dan takarar shugaban kasa a APC ya sauya sheka zuwa PDP

Dan takarar shugaban kasa a APC ya sauya sheka zuwa PDP

- Tsohon dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC, Cif Charles Udeogaranya ya sauya sheka zuwa jam’iyyar Peoples PDP

- Cif Udeogaranya a gangamin sauya shekar yace ya nemi yardan magoya bayansa don yin wannan yunkuri gabannin zaben 2019

- Yace sabuwar jam’iyyarsa ra PDP ta shirya karbar ragamar mulki a fadin kasar

Tsohon dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki, Cif Charles Udeogaranya a jiya ya sauya sheka zuwa jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), a wani taro da aka shirya a Lekki Phase 1, jihar Lagas.

Cif Udeogaranya a gangamin sauya shekar yace ya nemi yardan magoya bayansa don yin wannan yunkuri gabannin zaben 2019.

Dan takarar shugaban kasa a APC ya sauya sheka zuwa PDP

Dan takarar shugaban kasa a APC ya sauya sheka zuwa PDP
Source: Depositphotos

Yace sabuwar jam’iyyarsa ra PDP ta shirya karbar ragamar mulki a fadin kasar.

Ya yabama yan Najeriya a fadin kasar akan tarin goyon baya da biyayya da suke ba PDP.

KU KARANTA KUMA: Gwamnatin tarayya za ta saki N4bn don fanshon manyan farfesa da sakatarorin gwamnati

Yace PDP na kokarin ganin ta fitar da Najeriya daga mawuyacin halin da tattain arzikinta ya shiga.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel