Jama’a na zanga-zangar nuna damuwa da yawaitar kashe-kashe a Zamfara

Jama’a na zanga-zangar nuna damuwa da yawaitar kashe-kashe a Zamfara

Jama’a jihar Zamfara na gudanar da zanga-zanga akokarinsu na nuna damuwa da yawaitar kisan gilla da ake yiwa mutane a sassa daban-daban na jihar.

Ana gudanar da zanga-zangar ne a karamar hukumar Tsafe, da ke nisan kusan kilomita 50 da Gusau babban birnin jihar.

Rahotanni sun kawo cewa matasa da yan gudun hijira da suka kunshi mata da yara kanana sun toshe babbar hanyar da ke zuwa Gusau, tare da kone wasu gine-ginen gwamnati.

Jama’a na zanga-zangar nuna damuwa da yawaitar kashe-kashe a Zamfara

Jama’a na zanga-zangar nuna damuwa da yawaitar kashe-kashe a Zamfara
Source: UGC

Rundunar 'yan sandan jihar da ta tabbatar da faruwar al'amarin ta ce ta kama wasu daga cikin masu zanga-zangar.

Mazauna garin na tsafe na bayyana damuwa ne kan yadda masu gudun hijira ke ci gaba da tururuwa a yankin, suna guduwa sakamakon hare-haren da ake zargi yan bindiga da barayin shanu ke kai wa.

KU KARANTA KUMA: Gwamnatin tarayya za ta saki N4bn don fanshon manyan farfesa da sakatarorin gwamnati

Masu zanga-zangar sun bayyana cewa, sun gaji da halin ko-in-kula da hukumomi suke nunawa a kan rashin tsaro a jihar.

Shugaban karamar hukumar Tsafe Alhaji Abubakar Aliyu ya bayyana cewa, sama da mutum 40 ne suka rasa rayukansu a kauyuka daban-daban cikin mako biyu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel