Yan bindiga sun kashe jagoran APC da wasu 19 a Zamfara

Yan bindiga sun kashe jagoran APC da wasu 19 a Zamfara

- Yan ta’adda sun dawo da kai hare-hare a garuruwan jihar Zamfara

- Sun kashe mutane 20 ciki har da jigon jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na jihar, Alhaji Aliyu Abbas

- Yan ta’addan sun kai hari garin Magami dake karamar hukumar Maradun inda suka budewa marigayin wuta ya kuma mutu a nan take

Yan ta’adda sun dawo da kai hare-hare a garuruwan jihar Zamfara, inda suka kashe mutane 20 ciki har da jigon jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na jihar, Alhaji Aliyu Abbas, jaridar Leadership Hausa ta ruwaito.

‘Yan ta’addan sun kai hari garin Magami dake karamar hukumar Maradun inda suka budewa marigayin wuta ya kuma mutu a nan take, wani da aka yi abin a gabansa ya bayyana cewa, bayan da suka kashe Abbas ne suka kuma bude wuta a kan jama’a in da mutane 19 suka rasa ransu.

Yan bindiga sun kashe jagoran APC da wasu 19 a Zamfara

Yan bindiga sun kashe jagoran APC da wasu 19 a Zamfara
Source: Depositphotos

Sarkin Maradun, Alhaji Garba Tambari ya bayyana wa mukaddashin gwamnan da sauran manyan jami’a rundunonin tsaron jihar cewa, jami’an tsaron da ke yakar ‘yan ta’addan na dari-dari da ayyukansu, ba sa aikin da yadda ya kamata.

Ya yi mamakin yadda jami’an tsaron ke gudun yin gaba da gaba da ‘yan ta’addan a duk lokacin da suka kawo hari.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Buhari ya aika sakon Kirisimeti ga Kiristoci

Ya kuma kara da cewa, lokaci ya yi da jami’an tsaro za su yi azamar ganin kawo karshen ‘yan ta’addan a jihar zamfara gaba daya.

Sarkin ya kuma bayyana cewa, a haka yanzu garuruwa da kauyuka da daman a karkashin mulkin ‘yan ta’adda.

Shugaban karamar hukumar, Hon. Yahya Shehu ya nuna damuwarsa a kan ayyukan da jamoi’an tsaron ke yi a jihar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel