Karin aure da manoma keyi ya janyo hayayafar al'umma a Najeriya - Minista

Karin aure da manoma keyi ya janyo hayayafar al'umma a Najeriya - Minista

- An dora alhakin karuwar al'ummar Najeriya fiye da kima a kan manoman shinkafa

- Karamin ministan noma da raya karkara, Sanata Heineken Lokpobiri ya ce manoman suna kara aure suna haihuwan yara barkatai

- Lokpobiri ya ce gwamnati tana damuwa kan yadda adadin mutanen Najeriya ke karuwa a cikin kankanin lokaci

Karamin ministan noma da raya karkara, Sanata Heineken Lokpobiri ya dora wa manoman Najeriya laifi game da karuwar al'umma da ake samu a Najeriya.

The Sun ta ruwaito cewa ministan ya yi bayanin cewa manoman suna amfani da nasarorin da aka samu a fanin ayyukan noma domin kara auro mata tare da haihuwar yara wadda hakan ya janyo karuwar al'umma a kasar.

Monoma ke janyo hayayafar al'umma a Najeriya - Minista

Monoma ke janyo hayayafar al'umma a Najeriya - Minista
Source: Depositphotos

Legit.ng ta gano cewa ministan ya yi wannan furucin ne a yayin da ya ke tarbar wakiliyar International Fund for Agricultural Development (IFAD), Ms Ndine Gbossa a babban birnin tarayya, Abuja.

DUBA WANNAN: Gwamnatin tarayya ta fadi abinda ke janyo hare-haren ta'addanci a Zamfara da Kaduna

Idan ba a manta ba, ministan kasafin kudi da tsare-tsaren kasa, Udo Udoma ya ce karuwar al'umma da ake samu a Najeriya ne dalilin da yasa ake fama da rashin ayyukan yi a kasar.

A cikin wani sako da mai bashi shawara a kan kafafen watsa labarai, George Oji ya fitar, Ministan ya ce karuwar al'umma da aka samu a Najeriya ya wuce hasashen da majalisar dinkin duniya tayi na cewa za a samu mutane miliyan 200 a shekarar 2020.

"Abinda na gano shine akwai attajirai sosai daga cikin monama shinkafa a wasu jihohin Najeriya kuma wannan karin arzikin da suka samu yasa suna kara auren mata.

"Dama abu biyu suke son yi; Sun samu damar saukan farali a kasar Saudiyya domin yana daga burin dukkan musulmi ya tafi aikin hajji.

"Kuma 90% cikin wadanda suka tafi aikin hajji manoma ne; Manoman shinkafa ko manoman rogo da manoman masara da sauransu." inji shi.

Ministan ya ce gwamnatin tarayya tana matukar damuwa a kan yadda adadin al'ummar Najeriya ke karuwa wadda hakan ke janyo rashin samun abinci masu gina jiki musamman a tsakanin yara.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel