Yanzu Yanzu: Buhari ya aika sakon Kirisimeti ga Kiristoci

Yanzu Yanzu: Buhari ya aika sakon Kirisimeti ga Kiristoci

- Shugaban kasa Buhari ya jadadda burin samar da Najeriya mai inganci anan gaba

- Ya bayyana hakan a sakonn Kirisemeti da ya aikewa yan Najeriya

- Buhari yayiwa yan Najeriya alkawarin cewa gwamnatinsa za ta gudanar sa zabe na gaskiya da amana a shekara mai zuwa, cewa maganarsa kaifi daya ne

Shugaban kasa Mummadu Buhari ya jadadda burin samar da Najeriya mai inganci anan gaba, a sakon Kirisimeti da ya aikewa yan Najeriya.

A wani sako dauke da sa hannunsa, Buhari yace: “A koda yaushe kada mun manta cewa abunda ke gabanmu a matsayin kasa yafi duk wani abunda da muka fuskanta a baya inganci."

Yanzu Yanzu: Buhari ya aika sakon Kirisimeti ga Kiristoci

Yanzu Yanzu: Buhari ya aika sakon Kirisimeti ga Kiristoci
Source: Depositphotos

Kan haka yayiwa yan Najeriya alkawarin cewa gwamnatinsa za ta gudanar sa zabe na gaskiya da amana a shekara mai zuwa, cewa maganarsa kaifi daya ne.

“Alwashi da na dauka na jajirewa akan zabe na gaskiya da amana kuma mara rikici ba yaudara bane ko kuma wani alkawarin siyasa. Ina tsaye ne akan Magana na kaifi daya ne.

“Rantsuwa ne da ta ta’allaka akan ci gaban Najeriya, makoma da kuma kariya ga matasanmu da wadanda za’a Haifa anan gaba.

KU KARANTA KUMA: Buhari shugaba ne mai amana – Shugaban kungiyar Qadiriyya

“Mu fada ma duniya cewa babi shakka abu mai kyau na iya fitowa daga Najeria. Sannan zai faru, yayinda dukkanmu muka dadu domin ganin ya faru”, inji Buhari.

Sannan yayiwa Kiristocin Najeriya fatan alkhairi da bikin Kirisimeti cikin aminci, sannan ya bukai suyi koyi da koyarwar annabi Isah wajen wanzar da zaman lafiya tare da yafiya sannan ya bukaci suyi amfani da wannan dama wajen yiwa kasa addu’a.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel