Gwamnatin tarayya za ta saki N4bn don fanshon manyan farfesa da sakatarorin gwamnati

Gwamnatin tarayya za ta saki N4bn don fanshon manyan farfesa da sakatarorin gwamnati

- Gwamnatin tarayya ta shirya sakin naira biliyan hudu domin fara biyan cikakken albashi a matsayin fansho ga wasu rukunin masu ritaya

- Wadanda za su amfana sune manyan farfesa da sakatarorin gwamnati da suka yi ritaya

- Za’a fara biyansu cikakken albashin da suke karba kafin ritayarsu a matsayin kudin fansho

Gwamnatin tarayya ta shirya sakin naira biliyan hudu domin fara biyan cikakken albashi a matsayin mafi karancin fansho ga wasu rukunin masu ritaya a karkashin shirin tallafin fansho a karkashin dokar 2014, jaridar Punch ta ruwaito.

Wasu daga cikin farfesa da wadanda suka rike mukaman gwamnati a karkashin shirin fansho din da basu samun fansho daidai da albashinsu a lokacin da suke aiki za su fara karba fansho daidai da albashinsu, bincike ya nuna.

Gwamnatin tarayya za ta saki N4bn don fanshon manyan farfesa da sakatarorin gwamnati

Gwamnatin tarayya za ta saki N4bn don fanshon manyan farfesa da sakatarorin gwamnati
Source: Depositphotos

Wani babban jami’in hukumar fasho, wanda ya bayyana hakan ga majiyarmu, ya bayyana cewa hukumar ta kammala shiri domin fara biyan kudaden kamar yadda yake a dokar fansho na 2014.

KU KARANTA KUMA: Bana tsoron Buhari, Allah kadai nake tsoro – Gwamna Amosun

Yace: “Mun yi kasafin kudi sannan muna jira ne kawai gwamnati ta saki kudin. Naira biliyan hudu kawai muke bukata domin fara biyansu harda bashin da suke bi.

Yace da zaran gwamnati ta biya kudin toh za su fara biyan yan fansho din kudadensu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel