Kisan Badeh: An sako abokin shi da suke tare

Kisan Badeh: An sako abokin shi da suke tare

Wadanda suka kashe tsohon babban hafson tsaro na Najeriya, Air Cif Marshal Alex Badeh mai murabus sun sako abokinsa da su kayi garkuwa da shi kamar yadda Punch ta tabbatar.

An gano cewar san sako abokin Badeh ne bayan iyalansa sun biya kudin fansa wadda ya tasanma miliyoyin naira.

A sanarwa da 'yan sanda suka fitar da makon da ta gabata, ta ce, "Tsohon babban hafson tsaron ya samu rauni sakamakon harbinsa da akayi wadda ya yi sanadiyar mutuwarsa yayin da direbansa ya tsira da raunin harsashi sannan anyi awon gaba da abokinsa."

Majiyar Legit.ng ta gano cewa jami'an tsaro suna tunanin cewa kamar garkuwa da Badeh akayi niyyar yi da farko amma aka samu matsala shi yasa aka sako abokinsa bayan an biya kudin fansa.

Kisan Badeh: An sako abokin shi da suke tare

Kisan Badeh: An sako abokin shi da suke tare
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Gwamnatin tarayya ta fadi abinda ke janyo hare-haren ta'addanci a Zamfara da Kaduna

An kuma gano cewa an samu afkuwar sace mutane makamancin wannan a titin Keffi zuwa Abuja har sau biyu kafin kashe Badeh a cikin wata daya.

Wata majiya daga NAF ta shaidawa Punch cewa hukumar Sojin Saman Najeriya tare da 'yan sanda za su kira taron manema labarai bayan hutun Kirisimeti.

"A yayin da ake cigaba da bincike, iyalan abokin Badeh sun biya kudin fansa kuma an sako shi. Sai dai muna cigaba da bincike kuma muna samun nasara. Za mu sanar da al'umma abinda ake ciki bayan hutun Krisimeti," inji jami'in na NAF.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel