An kashe mutum 40 cikin mako 2 a Zamfara

An kashe mutum 40 cikin mako 2 a Zamfara

- Yan ta’adda sun hallaka akalla mutane 40 cikin mako biyu a yankin karamar hukumar Tsafe na jihar Zamfara

- Yan bindiga dai na ci gaba da addabar mutane a garuruwan Zamfara

- Hukumomin tsaro dai sun ce suna i gaba da aiki tukuru domin ganin sun kawo karshen wannan annoba

Wasu da ake zargin yan fashi da kuma masu garkuwa da mutane sun hallaka akalla mutane 40 a cikin mako biyu kacal a yankin karamar hukumar Tsafe da ke jihar Zamfara.

Yan fashi dai sun addabi al'umman Zamfara da yawan hare-hare duk da matakan da hukumomin tsaron Najeriya ke cewa suna dauka da nufin murkushe su.

A yammacin Asabar sai da suka hallaka akalla mutane 16 a kauyen Magamin Diddi na karamar hukumar Muradun da ke jihar.

An kashe mutum 40 cikin mako 2 a Zamfara

An kashe mutum 40 cikin mako 2 a Zamfara
Source: Depositphotos

Shugaban karamar hukumar Tsafe, Aliyu Abubakar Tsafe ya ce tsawon kwanaki uku ke nan 'yan ta'addan nakai farmaki a kauyen Asaula, inda rabin mutanensa suka tsere zuwa gudun hijira.

Hakazalika, duk a wannan dare sun kuma auka wa kauyen Sakiya, inda suka kashe mutane tare da sace mutum 11 ciki har mata guda uku.

KU KARANTA KUMA: Ta kare ma Najeriya idan har Buhari ya kara wasu shekaru 4 anan gaba – Peter Obi

Ya kara da cewa kusan kowanne dare sai sun shiga gari daya zuwa biyu, su kashe mutane, su yi garkuwa da wasu, kuma su kona dukiyoyinsu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel