Ta kare ma Najeriya idan har Buhari ya kara wasu shekaru 4 anan gaba – Peter Obi

Ta kare ma Najeriya idan har Buhari ya kara wasu shekaru 4 anan gaba – Peter Obi

- Peter Obi yace tattalin arzikin Najeriya zai ci gaba da tabarbarewa idan har Buhari ya ci gaba da mulki na tsawon wasu shekaru hudu anan gaba

- Da Dan takarar mataimakin shugaban kasa a jam’iyyar ta PDP ya kafa hujja da kasafin kudin 2019 da Buhari ya gabatar a gaban majalisar dokokin kasar

- Yace Najeriya ba za ta rayu ba idan Buhari ya aiwatar da shirye-shiryensa na daurawa talakawan Najeriya haraji

Peter Obi, dan takarar mataimakin shugaban kasa a jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), yace tattalin arzikin Najeriya zai ci gaba da tabarbarewa idan har shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ci gaba da mulki na tsawon wasu shekaru hudu anan gaba.

Da yake Magana a Lagas a ranar Asabar, 22 ga watan Disamba Obi ya kafa hujja da kasafin kudin 2019 da Buhari ya gabatar a gaban majalisar dokokin kasar a ranar Laraba da ya gabata.

Ta kare ma Najeriya idan har Buhari ya kara wasu shekaru 4 anan gaba – Peter Obi

Ta kare ma Najeriya idan har Buhari ya kara wasu shekaru 4 anan gaba – Peter Obi
Source: Depositphotos

A cewarsa, Najeriya ba za ta rayu ba idan Buhari ya aiwatar da shirye-shiryensa na daurawa talakawan Najeriya haraji, kamar yadda yake a kasafin kudin da aka gabatar wanda ya ta’allaka ne akan ciwo bashi.

Da yake lissafa abubuwan da dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP zai yi domin gyara lamarin idan har aka zabe shi akan mulki, Obi yace za’a mayart da hankali akan kananan masana’antu.

KU KARANTA KUMA: Gugar zana: Bayan Allah da Buhari wani kato baya bamu tsoro - Gwamnan APC

Yace gwamnatin Atiku zata dawo karfin gwiwar zuba jari sannan ta saukaka yadda ake kasuwanci a kasar domin habbaka tattalin arziki.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel