Atiku sun zargi Buhari da APC da kokarin cinnawa ‘Yan Majalisa EFCC da DSS

Atiku sun zargi Buhari da APC da kokarin cinnawa ‘Yan Majalisa EFCC da DSS

Ku na da labari cewa an yi Shugaban kasa Muhammadu Buhari ihu a majalisar tarayya lokacin da ya je gabatar da kasafin kudin shekara mai zuwa. Har yanzu wannan abu da aka yi yana cigaba da jawo ce-ce-ku-ce.

Fadar Shugaban kasa ta shirya kutin-gwila domin a daure wasu ‘Yan Majalisa – Buba Galadima

Injiniya Buba Galadima yace ana neman damke 'Yan Majalisan PDP
Source: Depositphotos

Kakakin kungiyar nan ta PPCO mai yakin neman zaben Atiku Abubakar watau Buba Galadima, ya bayyana cewa manyan jam’iyyar APC da kuma fadar shugaban kasa sun shirya daure ‘Yan majalisar da su kayi wa Shugaban kasa Buhari ihu.

Buba Galadima, wanda yana cikin masu magana da yawun bakin jirgin yakin neman zaben Atiku Abubakar a zaben 2019 ya tabbatar da cewa sun bankado shirin da ake yi na kama wasu ‘Yan majalisar hamayyar da su ka nunawa Buhari adawa.

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya fadawa jama'a su zabi mutanen kwarai zaben 2019

Injiniya Galadima yayi wannan ikirari ne a gaban ‘Yan jarida jiya Lahadi, a babban birnin tarayya Abuja. Galadima yace an fara rubuta sunan ‘yan majalisar da su ka rika yi wa Buhari ihu wancan makon, kuma za a mika sunayen su wajen EFCC.

Galadima ya nuna cewa ‘Yan Sanda ko Jami’an DSS da EFCC da Hukumar ICPC ko ma shugaban kasa ba su isa su kama wani ‘dan majalisa don yayi wa shugaban kasa bore ba. Galadima yace wannan aiki da ake kitsawa yana iya taba APC a 2019.

Injiniyan yake cewa mafi yawan abin da Buhari ya fada wajen gabatar da kasafin 2019 ba gaskiya bane. Haka kuma ya kara da cewa Shugaban kasar ya sabawa dokar zabe, a sakamakon makudan gudumuwar da ya karba daga hannun manoma.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel