Kamfen: Gwamnatin Akwa Ibom ta bayyana dalilin hana Buhari amfani da filin wasan jihar

Kamfen: Gwamnatin Akwa Ibom ta bayyana dalilin hana Buhari amfani da filin wasan jihar

Gwamnatin Akwa Ibom ta ce shugaban kasa Muhammadu Buhari ba zai samu damar yin amfani da filin wasa na kasa da kasa dake Uyo, babban birnin jihar, domin kaddamar da yakin neman zabensa ranar Juma'a ba.

A ranar Juma'a ne shugaba Buhari zai ziyarci jihar Akwa Ibom domin kaddamar da yakin neman zabensa a jihar, kuma jam'iyyar APC ta nemi izinin gwamnatin jihar domin yin amfani da babban filin wasa na Godswill Akpabio.

Sai dai gwamnatin jihar ta Akwa Ibom ta sanar da shugaba Buhari cewar sai dai ya yi amfani da karamin filin na garin Uyo ba babban filin wasa na Godswill Akpabio ba kamar yadda ya nema.

Kamfen: Gwamnatin Akwa Ibom ta bayyana dalilin hana Buhari amfani da filin wasan jihar

Taron gangami APC
Source: Depositphotos

Da yake bayyana dalilin hana Buhari amfani da filin wasan, kwamishinan wasanni a jihar Akwa Ibom, Monday Uko, ya ce, "za a fara gasar cin kofin Firemiya na kasa a ranar 13 ga watan Janairu, 2019, a saboda haka ba zamu iya bari taron jama'ar da zasu halarci kamfen din shugaban kasa su lalata mana ciyawar filin wasa ba, musamman a daidai wannan lokaci da kungiyar kwallon kafa ta Akwa United ke buga wasannin gwaji ba.

"Kazalika kamfanin Julius Berger dake aikin kula da filin ya bayar da shawarar cewar bai kamata a takura wa ciyawar filin dake shan wahalar yanayi mai tsanani ba."

DUBA WANNAN: An kone motocin yakin neman zabe Buhari 2 a jihar PDP

Mista Uko ya ce ya zama dole su fito fili suyi bayani domin tuni wasu 'yan siyasa a jihar sun fara bawa lamarin wata fassara ta daban. Sannan ya kara da cewa hatta taron kiristoci da suka shirya zasu yi a filin wasa na Godswill Akpabio bai samu yiwu ba, sai a karamin filin wasa har suka yi taronsu.

Kokarin jin ta bakin Ini Okopido, shugaban APC ko wani jigo a jam'iyyar a jihar Akwa Ibom bai samu ba har lokacin da ka kammala wannan rahoto.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel