Obasanjo ya fadi wasu da mutane da Allah ba zai bari su mulki Najeriya ba

Obasanjo ya fadi wasu da mutane da Allah ba zai bari su mulki Najeriya ba

A jiya, Asabar, ne tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya ce Najeriya ta dukkan 'yan kasa ce tare da bayyana cewar Allah ba bar wasu 'yan tsirarun mutane "marasa tausayi" su mulki Najeriya ba.

Obasanjo ya yi wannan kalami ne a wurin bikin taya Farfesa Ango Abdullahi murnar cika shekaru 80 a duniya da aka yi a gonar sa dake Basawa a garin Zaria.

A taron taya Farfesan murna da iyalin Abdullahi Kwasau suka shirya, Obasanjo ya yi tsokaci kan matsalolin tsaro da suka dabaibaye kasar nan.

Ya ce dattijai irinsa ba zasu bar al'amuran kasar nan su tabarbare ba, domin yin hakan tamkar dasa tsiron da zai rusa Najeriya ne.

Obasanjo ya fadi wasu da mutane da Allah ba zai bari su mulki Najeriya ba

Obasanjo
Source: UGC

Ya kara da cew: "an ce mana an gama da matsalar Boko Haram bayan har yanzu tana nan. Ya kenan zamu yi? kowa zai iya zama mai tayar da hankalin jama'a. Tashin hankali a Najeriya a Najeriya har ya kai ga sace matasa a ranar da zasu yi aure.

DUBA WANNAN: Kasafin 2019: Ka nemi yafiyar 'yan Najeriya a kan karyar da ka shirga - PDP ta fadawa Buhari

Matukar al'amura basa tafiya daidai a kasar mu, to akwai bukatar mu hada kai domin ganin komai ya tafi daidai. Babu wani mutum guda da zai ce Najeriya tasa ce, Allah ba zai bar hakan ta faru ba."

A nasa bangaren, Farfesa Ango ya ce taron taya shi murnar zai kara dankon zumuci a tsakanin iyalin Abdullahi Kwasau.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel