Kilu ta za bau: Mutanen kauyukan da aka kashe Alex Badeh za su sha tambayoyi

Kilu ta za bau: Mutanen kauyukan da aka kashe Alex Badeh za su sha tambayoyi

Rundunar sojojin saman Najeriya sun lissafa jama'ar dake a kauyukan da ke kusa da inda aka kashe tsohon Hafsan sojin Najeriya Alex Badeh a cikin wadanda za su sha tambayoyi a cigaba da bincike da suke yi kan kasan na tsohon shugaban na su da aka yi a satin da ya gabata.

Jami'in hulda da jama'a na rundunar ne dai Air Commodore Ibikunle Daramola ya bayyanawa majiyar mu hakan a wata fira da yayi da wakilin su yayin da kuma ya bayar da tabbacin cewa jami'an su za su tabbatar da cewa sun zakulo wadanda suka yi kisan.

Kilu ta za bau: Mutanen kauyukan da aka kashe Alex Badeh za su sha tambayoyi

Kilu ta za bau: Mutanen kauyukan da aka kashe Alex Badeh za su sha tambayoyi
Source: Twitter

Legit.ng Hausa dai ta tuna cewa a ranar Talata ne da ta gabata da marece wasu 'yan bindiga da ba'asan ko suwaye ba suka kashe Marigayi Alex Badeh din a kan hanyar sa ta zuwa gona.

A wani labarin kuma, Wani mai maganin gargajiya da kan yi shigar burtu yayi mutane fashi da makami ya gamu da gamon shi yayin da ya shiga hannun jami'an 'yan sandan Najeriya.

Mai maganin gargajiyar dai mai suna Abdullahi Mudi, kamar yadda muka samu ya shiga hannun 'yan sandan ne tare da abokin tafka ta'asar sa mai suna Christopher Illia a wurare daban-daban a garin Abuja.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel