Ta zarce: Wata kila shugaba Buhari ya karawa shugaban 'yan sanda wa'adin mulki

Ta zarce: Wata kila shugaba Buhari ya karawa shugaban 'yan sanda wa'adin mulki

Ana tunanin wata kila shugaban kasa, Muhammadu Buhari zai karawa shugaban rundunar 'yan sandan Najeriya, Sifeto Janar Ibrahim Idris wa'adin mulki na kimanin watanni shidda nan ba da dadewa ba.

Wannan dai na zuwa ne biyo bayan zuwa karshe da wa'adin mulkin sa tare da kammala aikin sa na dan sanda da zai cika a ranar 3 ga watan Janairu na shekara mai kamawa lokacin da zai cika shekarun sa 35 a aikin sa.

Ta zarce: Wata kila shugaba Buhari ya karawa shugaban 'yan sanda wa'adin mulki

Ta zarce: Wata kila shugaba Buhari ya karawa shugaban 'yan sanda wa'adin mulki
Source: Depositphotos

KU KARANTA: Ba wanda zai kara shiga rigar Buhari a 2019

Legit.ng Hausa ta samu cewa sai dai akwai yiwuwar shugaban kasar ya kara wa'adin na sa biyo bayan kamun kafa da yayi tayi a wajen wasu makusantan shugaban kasar da nufin su sa baki a kara masa wa'adin.

Sai dai kuma dai tuni wannan yunkurin na karin wa'adin mulki ya soma samun tangarda daga kungiyoyi yayin da wata kungiya ta gamayyar jam'iyyun siyasa a Najeriya mai suna Coalition of United Political Parties (CUPP) ta yi barazanar zuwa kotu idan har shugaban kasar ya kara masa wa'adin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel