Dalilin da yasa muka daina goyon bayan Atiku - shugaban kungiyoyi 145

Dalilin da yasa muka daina goyon bayan Atiku - shugaban kungiyoyi 145

A cikin makon da ya gabata ne gamayyar wasu kungiyoyi fiye da 145 suka bayyana janye goyon bayansu ga dan takarar shugaban kasa a karkashin jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, tare da bayyana goyon bayansu ga takarar shugaban kasa Muhammadu Buhari a karkashin jam'iyyar APC.

Shugaban gamayyar kungiyoyin, Bello Osaretin, ya bayyana dalilinsu na daukan wannan mataki a wata doguwar hira da ya yi da kamfanin jaridar The Nation.

A cewar Osaretin, sun daina goyon bayan Atiku da PDP ne saboda sun ga cewar har yanzu basu koyi darasi daga abinda ya faru a baya ba.

Osaretin ya ce PDP ba da gaske take a kan son dawowar mulkin Najeriya hannunta ba saboda ta sake cigaba da nuna halayen da suka jawo mata faduwa zabe a shekarar 2015 da jam'iyyar ta kayar da ita.

"Sun ce sun canja, sun zama 'yan siyasa na gaskiya amma kuma sun cigaba da cushe da kakaba 'yan takara, sannan sun cigaba da nuna halin nan na "a ci moriyar ganga, a yasar da kwaurwenta" da kuma yin butulci ga 'ya'yanta da suka yi mata wahala.

Dalilin da yasa muka daina goyon bayan Atiku - shugaban kungiyoyi 145

Atiku
Source: Depositphotos

"Wadannan dalilai da wasu da dama suka sa muka yanke shawarar barin jam'iyyar tare da dan takarar ta. Yanzu bama tare da PDP ko Atiku.

"Mun bar Atiku saboda halin "ko in kula" da yake nuna wa kungiyoyin mu da kuma yadda ake nuna kabilanci da bangaranci a bawa kungiyoyin yakin neman zabensa muhimmanci," a kalaman Osaretin.

DUBA WANNAN: Al'ajabi: Wata mata ta fara aman N500 bayan dan damfara ya yi tsafi da ita

Da yake amsa tambayar cewar dama tun asali basa goyon bayan Atiku, kuma duk abinda suke yi rudu ne irin na siyasa, sai Osaretin ya kada baki ya ce, "Atiku da shugabannin yakin neman zabensa sun san mu. Mun yiwa Atiku aiki tukuru, mun tuntubi jama'a da dama, musamman daliget, domin nemawa Atiku goyon. Tun 2011 muke goyon bayan Atiku, amma yanzu mun fusata saboda rashin nuna sanin muhimmancin mu, saboda ana amfani da mu a jefar sai bukatar mu ta taso a sake nemo mu."

Osaretin ya kara da cewar sun yanke shawarar goyon bayan shugaba ne saboda irin aiyukan alheri da ya yi a lungu da sakon Najeriya, yana mai bayyana cewar tabbas shugaban Buhari zai lashe zaben shekarar 2019.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel