Gobe fadar Shugaban kasa za ta karbi rahoto game da Shugaban NHIS

Gobe fadar Shugaban kasa za ta karbi rahoto game da Shugaban NHIS

Kwamitin da aka nada domin ya gudanar da bincike a game da Shugaban Hukumar NHIS, Farfesa Usman Yusuf ya kammala aikin sa, kuma ana sa rai cewa za a mikawa Shugaban kasa rahoton gobe.

Gobe fadar Shugaban kasa za ta karbi rahoto game da Shugaban NHIS

Shugaba Buhari ya sa a binciki Shugaban Hukumar NHIS
Source: Depositphotos

Jaridar Punch ta rahoto cewa a Ranar Litinin din gobe ne kwamitin da yayi aiki a kan zargin da ke wuyan Farfesa Usman Yusuf wanda ke shugabantar Hukumar inshore ta lafiya, zai gabatarwa Gwamnatin Tarayya aikin da yayi.

Kwamitin za ta mikawa Sakataren Gwamnatin Najeriya watau Mista Boss Mustapha aikin da tayi bayan kusan watanni 2. Sakataren wannan kwamiti da aka kafa, Jumai Ndako ta bayyanawa ‘Yan Jarida wannan a karshen makon nan.

KU KARANTA: Buhari ya jagoranci taron kasashen Afrika a matsayin sa na Shugaban ECOWAS

An dai dauki lokaci ana wannan aiki inda wani babban Jami’i a ofishin Sakataren Gwamnatin kasar ya bayyana mana cewa bacin lokacin da aka samu ya fito ne daga wajen kwamitin da aka daurawa nauyin gudanar da binciken na musamman.

Ana tsoron cewa ana iya yin watsi da binciken da aka yi a cewar wani jami’in Gwamnatin Tarayya. Ndako ta bayyana cewa sun dauki dogon lokaci kafin su soma aiki bayan an kafa kwamitin na su bayan an dakatar da Farfesa Yusuf daga aiki.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel