Buratai ya saka baki a rigimar UNICEF da rundunar sojin Najeriya

Buratai ya saka baki a rigimar UNICEF da rundunar sojin Najeriya

Hukamar sojin Najeriya ta kara jaddada niyyarta ta hada kai da duk wata kungiyar cikin gida ko waje domin aikin taimakon jama'ar fa rikicin Boko Haram ya shafa a arewa maso gabashin Najeriya.

Shugaban rundunar soji, Laftanal janar Tukur Yusuf Buratai, ne ya bayyana hakan yayin wata tattaunawa da kungiyar editocin jaridu ta shirya a Maiduguri.

Da yake karin haske a kan sabanin da ya shiga tsakanin rundunar soji da kungiyar agaji ya kasa da kasa (UNICEF), Buratai ya ce yanzu komai ya wuce, sun sulhunta.

"Ina tabbatar maku cewar yanzu babu sauran rashin jituwa tsakanin kungiyar UNICEF da rundunar soji.

"Na takaita maku magana, zamu yi aiki tare da kungiyar da ragowar kungiyoyin agaji dake bayar da tallafi ga jama'a.

Buratai ya saka baki a rigimar UNICEF da rundunar sojin Najeriya

Buratai
Source: Depositphotos

"Bai kamata tun farko mu samu sabani ba, amma wasu lokutan dole a dauki wasu matakai domin cimma wani sakamako," a cewar Buratai.

Sannan ya cigaba da cewa, "muna sane da nauyin dake wuyan mu a idon duniya duk da hakan kan jawo wasu matsaloli ga aiyukan dakarun soji.

DUBA WANNAN: Hoton kwamandan Boko Haram da Abba Kyari ya kama a Legas

"Ina mai farincikin cewar mun daidaita sabanin da ya shiga tsakani, bamu hana UNICEF da ragowar kungiyoyin agaji yin aikinsu ba," a kalaman Buratai.

Buratai ya ce yana fatan abinda ya faru ba zai sake maimaita kansa ba, sannan ya kara da cewar jami'an soji na bayar da gudunmawa yayin gudanar allurar rigakafi a yankin arewa maso gabas.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel