Hatsarin Mota ya salwantar da rayukan Mutane 2 a jihar Ogun

Hatsarin Mota ya salwantar da rayukan Mutane 2 a jihar Ogun

Hukumar kiyaye aukuwar hadurra ta kasa, Federal Safety of Nigeria Corps, FRSC, ta bayar da sanarwar cewa, wani mummunan hatsarin mota ya salwantar da rayukan Mutane biyu tare da jikkatar wasu biyun a yankin Idiroko na jihar Ogun.

Hatsarin Mota ya salwantar da rayukan Mutane 2 a jihar Ogun

Hatsarin Mota ya salwantar da rayukan Mutane 2 a jihar Ogun
Source: Depositphotos

Majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, hatsarin da ya auku a tsakanin motoci biyu ya salwantar da rayukan mutane biyu yayin da wasu mutane suka jikkata daura da unguwar Animashun da ke jihar Ogun a Kudancin Najeriya.

Shugaban hukumar reshen jihar Ogun, Mista Adekunle Oguntoyinbo, shine ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai na kamfanin dillancin labarai na kasa da cewa, tsautsayin ya auku ne da misalin karfe 5.30 na Yammacin ranar Asabar din da ta gabata.

An killace gawar wadanda suka riga mu gidan gaskiya a babban asibitin Ifo na birnin Abeokuta yayin da wadanda suka jikkata ke ci gaba da samun kulawa a asibitin Sango Ota.

KARANTA KUMA: 2019: Sanatocin Kasar Amurka sun daura damarar tabbatar da zabe na gaskiya a Najeriya

Mista Oguntoyinbo, ya gargadi masu ababen hawa akan kiyaye dokokin zirga-zirga da sufuri akan manyan hanyoyi tare da kauracewa tsala guda da ya wuce ka'ida musamman a wannan lokuta na shagulgulan Kirsimeti da bukukuwan karshen shekara.

Cikin wani rahoton mai nasaba da wannan, jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, wani mummunan hatsarin mota ya salwantar da rayukan Mutane 8 a babbar hanyar Jhajjar da ke yankin Haryana a kasar Indiya.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel