2019: Sanatocin Kasar Amurka sun daura damarar tabbatar da zabe na gaskiya a Najeriya

2019: Sanatocin Kasar Amurka sun daura damarar tabbatar da zabe na gaskiya a Najeriya

- Amurka ta bayyana ruwa da tsakin ta kan zaben kasa Najeriya na 2019

- Sanatoci hudu na majalisar tarayya Amurka sun ce dole a tabbatar da dimokuradiyya a Najeriya yayin zaben 2019

- Kasar Amurka ta bayyana fargabarta dangane da yadda adawar siyasa ta yi matukar tsanani a Najeriya

Mun samu cewa a wannan mako, wasu Sanatoci hudu na majalisar tarayyar kasar Amurka, sun fito kwansu da kwarkwata gami zage dantsen su domin tabbatar da an gudanar da zaben na lumana da kwanciyar hakali yayin babban zaben kasar Najeriya na badi.

Sanatocin sun jaddada cewa, dole Najeriya ta ci gaba da tabbatuwa bisa tafarkin zaman lafiya tare da koyi da lumanar da ta kasance wajen mika mulki hankali kwance yayin zaben 2015 da ya gabata cikin kasar nan.

Kamar yadda majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito, Sanatocin hudu da suka tabbatar da diga-digan su gami da tsayuwar daka ta bayyana ruwa da tsakin su kan zaben 2019 sun hadar da Jeff Flake, Cory Booker, Johnny Isakson, da kuma Christopher Co*ns.

Mataimakin sakataren gwamnatin Amurka kan harkokin nahiyyar Afirka; Tibor Nagy

Mataimakin sakataren gwamnatin Amurka kan harkokin nahiyyar Afirka; Tibor Nagy
Source: UGC

Cikin wata wasika da Sanatocin suka aike da ita zuwa ga mataimakin sakataren gwamnatin Amurka kan harkokin kasashen Afirka, Tibor Nagy, sun jaddada tsayuwar dakan gwamnatin kasar su na tabbatar da kwararar romon dimokuradiyya yayin zaben 2019.

Gwamnatin Amurka ta dukufa wajen bayar da muhimmiyar gudunmuwa a zaben Najeriya na badi kasancewar ta madubin dubawa ga sauran kasashen nahiyyar Afirka kamar yadda wasikar Sanatocin ta bayyana.

KARANTA KUMA: Yajin Aiki: Gwamnatin tarayya ba ta nemi a sulhunta ba - ASUU

Kazalika sun bayyana fargabar su dangane da yadda adawar siyasa ta dauki wani sabon salo na tsananin gaske da muddin ba a fargaba za ta kawo nakasun zaman lafiya tare da barazana ta rikici ga tarzoma.

Jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, Dan majalisa mai wakilcin kananan hukumomin Kiru da Bebeji na jihar Kano, Honarabul Abdulmumini Jibril, ya bayar da gudunmuwar Motoci 150 domin yakin neman zaben shugaban kasa Muhammadu Buhari da kuma gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel