Dalilin da yasa tsofin Janar na Najeriya basa son Buhari - Ambasada Ibrahim Kasi

Dalilin da yasa tsofin Janar na Najeriya basa son Buhari - Ambasada Ibrahim Kasi

- Tsohon jakadan Najeriya a kasar Ukraine, Ibrahim Kasai ya yi bayanan wasu dalilai da suka sa tsofin janar na Najeriya basa tare da shugaba Buhari

- Kasai, ya ce Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP, ba zai hana Buhari cin zaben 2019 ba

- Ambasada Kasai ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da jaridar the sun

Tsohon jakadan Najeriya a kasar Ukraine kuma mamba a kwamitin amintattu na yakin neman zaben shugaba Buhari, Ibrahim Kasai, ya ce Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP, ba zai iya yin galaba a kan Buhari ba a zaben shekarar 2019.

A wata hira da ya yi da jaridar Sun, Kasai ya ce tsofin Janar na soji sun dade suna daukar Najeriya tamkar wata gona da suka mallaka bayan dukkan 'yan kasa na da hakki a Najeriya.

Dalilin da yasa tsofin Janar na Najeriya basa son Buhari - Ambasada Ibrahim Kasi

Ambasada Ibrahim Kasai
Source: Facebook

Da aka tambaye shi ko mai yake tunanin ya jawo rashin jituwa tsakanin Buhari da tsofin Janar din kasar nan, sai ya ce, "na sha fada cewar tsofin Janar din kasar nan 'yan kasuwar man fetur ne dake jin tsoron cewar shugaba Buhari ba zai sabunta lasisin rijiyoyin man fetur da suka mallaka ba. Su wadannan tsofin Janar na adawa da Buhari ne domin kawai kare kasuwancinsu, wannan shine abinda ke faruwa."

DUBA WANNAN: 2019: Tsarin PDP ya fi na APC - Saraki

Da aka kara tambayar Ambasada Kasai a kan cewar ko yana nufin Janar Obasanjo, Babangida da TY Danjuma na fada da Buhari ne a kan bukatar kansu ba ta Najeriya ba, sai ya kada baki ya ce, "me zai hana idan suka ga za a raba su da abinda suke samu. Ai dama shugaba Buhari bai ce zai hana su yin kasuwanci ba, abinda yake magana shine; dukiyar Najeriya ta dukkan 'yan kasa ce, ba wasu tsirarun mutane ba."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel