Kasafin 2019: Ka nemi yafiyar 'yan Najeriya a kan karyar da ka shirga - PDP ta fadawa Buhari

Kasafin 2019: Ka nemi yafiyar 'yan Najeriya a kan karyar da ka shirga - PDP ta fadawa Buhari

Kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam'iyyar PDP (PPCO) ya zargi shugaba Buhari da kokarin yaudarar 'yan Najeriya a kasafin kudin da ya gabatar gaban majalisa a ranar Laraba ta makon jiya.

Jam'iyyar ta PDP ta bukaci shugaba Buhari ya nemi afuwar 'yan Najeriya bisa yin karyar kammala aiyukan da ba a kammala su ba.

A jawabin da jam'iyyar PDP ta saki ta bakin kakakinta, Kola Ologbondiyan, ta ce shugaba Buhari ya dogara da alkaluman bogi domin yaudarar 'yan Najeriya yayin gabatar da kasafin kudin shekarar 2019.

"Binciken tabbatar da gaskiyar maganganun shugaba Buhari ya nuna cewar wasu daga cikin aiyukan da ya yi ikirarin kammala su, basu kammalu ba yayin da wasu ma babu su.

Kasafin 2019: Ka nemi yafiyar 'yan Najeriya a kan karyar da ka shirga - PDP ta fadawa Buhari

Kola Ologbondiyan
Source: Depositphotos

"Daga cikin misalan irin wadannan aiyuka da ba a kammala su ba akwai batun kammala aikin Dam din Ugwashi-Uku a jihar Delta. Bincike ya tabbatar da cewar tun shekarar 2015 aka yi watsi da aikin, yanzu haka zancen da ake yi hatta hanyar da zata kai ga Dam a lalace take," a cewar jawabin PDP.

DUBA WANNAN: 2019: Tsarin PDP ya fi na APC - Saraki

Ko a jiya, Asabar, sai da tsohon gwamnan jihar Ekiti, Mista Ayodele Fayose, ya ce 'yan Najeriya ba zasu taba mantawa da shugaba Buhari ba saboda yadda ya lalata tattalin arzikin Najeriya da kuma karfafa kabilanci a cikin tafiyar da gwamnati.

Fayose, jagoran yakin neman zaben PDP a yankin kudu maso yamma, ya ce: "bayan yakin basasa, ba a taba samun wani lokaci da aka kashe dakarun soji a Najeriya ba kamar yadda take faruwa a karkashin gwamnatin Buhari ba."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel