Shugaban Najeriya Buhari ya jagoranci taron Kungiyar ECOWAS a Abuja

Shugaban Najeriya Buhari ya jagoranci taron Kungiyar ECOWAS a Abuja

Shugaba Muhammadu Buhari, ya jagoranci babban taron Kungiyar ECOWAS na kasashen Afrika ta Yamma da aka yi a babban Birnin tarayya Abuja. Taron da aka yi jiya shi ne zaman Kungiyar na 24.

Shugaban Najeriya Buhari ya jagoranci taron Kungiyar ECOWAS a Abuja

An gudanar da taron Kungiyar ECOWAS jiya a Garin Abuja
Source: Facebook

Shugaba Buhari na Najeriya ya zauna da shugabannin kasashen Afrika inda ya tattauna game da batun wanzar da zaman lafiya da samar da tsaro. Buhari yace rikicin ta’addanci ya zama babban cikas wajen cigaban tattalin arziki.

Muhammadu Buhari yayi kira ga shugabannin da ke makwabtaka da Najeriya su yi na sub akin kokarin wajen ganin an kawo karshen ta’addanci a Yankin Nahiyar. A cewar sa, ta’addanci yana ruguje duk wata nasara da ake samu

Shugaban kasar Najeriyar wanda shi ne Shugaban ECOWAS yace kokarin da yake yi wajen ganin an samu zaman lafiya yana tasiri a Nahiyar ganin yadda abubuwa su ka lafa a a Kasar Guinea Bissau, Togo da kuma Kasar Mali.

KU KARANTA: Babban Sojan da aka kashe ya gana da na kusa da Buhari daf da zai mutu

Wadanda su ka halarci wannan taro da aka yi sun hada da; Jean-Claude Kassi Brou; Muhammadu Buhari; Gnassingbé na kasar Togo Togo; da kuma Shugaba Alpha Condé na Kasar Guinea da Ibrahim Boubacar Keïta na Mali.

Buhari ya bayyana cewa dole kowane shugaba yayi bakin kokarin sa wajen ganin an yi maganin ‘Yan ta’adda a yammacin Afrika. Buhari ya kuma nemi kasashen su rika biyan kudin da aka sab aba ECOWAS a matsayin gudumuwa.

Nan da 2020, Kungiyar ta ECOWAS tana da burin ganin kasashen na Yammacin Afrika sun samu hadin-kai. Wakilin majalisar dinkin duniya na Yankin Afrika, Mohammed Ibn Chambas, yana cikin wadanda su kayi jawabi a wajen taron.

.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Mailfire view pixel