Yadda Shehu Sani zai kara a zaben 2019 wajen komawa Majalisar Dattawa

Yadda Shehu Sani zai kara a zaben 2019 wajen komawa Majalisar Dattawa

Mun samu labari daga Jaridar Daily Trust cewa akwai akalla ‘Yan takara 24 da su ka fito neman kujerar Sanatan Kaduna ta tsakiya a majalisar dattawa. Yanzu haka fitaccen Sanatan nan, Shehu Sani ne ke rike da wannan kujera.

Yadda Shehu Sani zai kara a zaben 2019 wajen komawa Majalisar Dattawa

Kujerar Kwamared Shehu Sani tana rawa a Kaduna
Source: UGC

Garuruwan da ke cikin wannan Yanki sun hada da Kaduna ta Arewa da Kaduna ta kudu a cikin Garin Kaduna sannan kuma da Garuruwan Igabi, Chikun, da Kajuru. Haka kuma wannan Mazaba ta hada har da Giwa da Birnin Gwari.

A baya irin su Sanata Marigayi Mukhtar Mohammed Aruwan, da Kabiru Jibril da kuma Janar Sani Saleh, sun rike wannan kujera kafin Kwamared Shehu Sani. A zaben 2019, wannan kujera ta na cikin wanda jama’a su kayi ca a kan ta.

Manyan ‘Yan takarar da za su fafata a zaben 2019 wajen neman kujarar Sanatan tsakiyar Kaduna sun hada da Shehu Sani wanda yake ikirarin fafatuka domin Talaka, da kuma Uba Sani wanda yake goyon bayan Buhari da El-Rufai sai Lawan Adamu wanda ake yi wa kallon na Matasa.

KU KARANTA: Babu abin da Gwamnatin Buhari ta tsinana – inji Shehu Sani

1. Shehu Sani

Sanata Shehu zai yi kokarin zarcewa a kan wannan kujera a Jam’iyyar sa ta PRP. Sanatan ya bar APC ne kwanaki bayan ya gaza samun tikitin takara. Rikicin Sanatan da Gwamnan Jihar ta sa dole ya sauya-sheka.

2. Uba Sani

Gwamna Nasir El-Rufai yana tare da babban Hadimin sa, Uba Sani a zaben Sanatan Kaduna ta tsakiya a 2019. El-Rufai ne yayi yadda yayi wajen ganin Mai ba sa shawara a kan harkokin siyasar ya samu tutar APC.

3. Lawal Adamu

Lawal Adamu, Matashi ne wanda ya tsere daga APC ya dawo PDP kwanakin baya. Adamu yayi yunkurin takarar shugaban karamar hukuma amma bai iya yin nasara a APC ba. Matasa na yi wa ‘Dan takarar lakabi da Mr. LA.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel