Afenifere ta karyata cewa ta yi wa Buhari mubaya’a a zaben 2019

Afenifere ta karyata cewa ta yi wa Buhari mubaya’a a zaben 2019

Mun ji labari cewa Kungiyar nan ta Afenifere wanda ke kare manufofin Yarbawan Kasar nan, ta fito tayi maza ta karyata cewa ta na tare da Shugaba Muhammadu Buhari a zaben shekara mai zuwa na 2019.

Afenifere ta karyata cewa ta yi wa Buhari mubaya’a a zaben 2019

Ba mu ce mu na goyon bayan Buhari ya zarce ba - Kungiyar Yarbawa
Source: UGC

Kungiyar Afenifere ta bayyana cewa Asiwaju Bola Tinubu wanda jigo ne a Jam’iyyar APC, shi ya fara kitsa cewa sun yi wa Buhari mubaya’a a kan Atiku Abubakar. Wata jarida ta rahoto wannan a Ranar Juma’ar da ta wuce.

An rahoto cewa manyan Dattawan Kungiyar ta Afenifere irin su Sanata Ayo Fasanmi sun zauna da manyan Kasar Yarbawa irin su Tajudeen Olusi, Prince Biodun Ogunleye; Dr. Abayomi Fini da Omololu Olunloyo a Ibadan.

Mai magana da yawun bakin Kungiyar Yarbawan, Yinka Odumakin, ya caccaki Bola Tinubu, wanda a cewar sa shi ya shirya wannan aiki. Odumakin yayi tir da wannan aiki da tsohon Gwamnan na Legas, Bola Tinubu yayi.

KU KARANTA: NASS tayi kira ga ‘Yan Majalisa su ruga su nemi gafarar Buhari

Odumakin yace yayi mamakin jin yadda Tinubu wanda a baya, yayi kaca-kaca da wannan Kungiya zai fito ya ci albasa da yawun su. Kakakin wannan Kungiya yake cewa a baya Tinubu yayi watsi da su sai da ya ga zabe ya karaso.

Cif Odumakin yace kungiyar ba ta san da zaman wadannan mutane da su ka yi magana a game da zaben 2019 da yawun su ba. A cewar Odumakin, Fasakin ne kurum ‘Dan Kungiyar, kuma da shi Jagororin APC su kayi amfani.

Kungiyar Afenifere ta nuna cewa za ta marawa duk ‘Dan takarar da yake goyon bayan an sauyawa tsarin Najeriya da tsarin mulkin fasali ne a zabe mai zuwa. Kungiyar tace za ta fitar da matsayar ta idan ta gana da sauran Kungiyoyi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Mailfire view pixel