Yajin Aiki: Gwamnatin tarayya ba ta nemi a sulhunta ba - ASUU

Yajin Aiki: Gwamnatin tarayya ba ta nemi a sulhunta ba - ASUU

Rahotanni da ke samun jaridar Legit.ng na nuni da cewa, kungiyar malaman jami'o'in Najeriya ta ASUU, ta bayyana hasashen ta dangane da yajin aikin da ta afka a fadin kasar nan tun a ranar 5 ga watan Nuwamba, inda ta ce gwamnatin tarayya ba ta bayar da wani muhimmanci ba na neman sulhu.

Shugaban kungiyar reshen jami'ar Calabar, Dakta Tony Eyang, shine ya bayyana hakan a ranar Juma'ar da ta gabata da cewa, ko kadan gwamnatin tarayya ba ta dauki sulhun tsakanin ta da kungiyar da wani muhimmanci ba.

Yajin Aiki: Gwamnatin tarayya ba ta nemi a sulhunta ba - ASUU

Yajin Aiki: Gwamnatin tarayya ba ta nemi a sulhunta ba - ASUU
Source: Depositphotos

Dakta Eyang ya bayyana hakan ne biyo bayan rashin haifar da wani tasiri na zaman tattauna da suka gudana sau da dama tsakanin kungiyar da kuma wakilan gwamnatin tarayya a karo daban-daban.

Ya ce rashin daya daga cikin bukatun kungiyar ya tabbatar da cewa gwamnatin tarayya ba ta dauke su da wani muhimmanci ba, duba da irin alkawurran da dauka a baya.

KARANTA KUMA: Buhari zai mika mulkin Najeriya zuwa ga Kudu maso Yamma a 2023 - Osinbajo

Kungiyar ASUU a ranar Larabar da ta gabata ta bayyana cewa, sauran kiris ta rattaba hannu kan wata yarjejeniya domin kawo karshen yajin aikin sai baba-ta-gani da ta afka makonni da suka shude.

Sai dai Dakta Eyang ya ce ba nan gizo yake saka ba, tabbatar da alhinin wannan yarjejeniya shine dahir domin kuwa hakan ta faru sau da dama ba tare da haifar wani tasiri ba. Ya ce a dai yi mu gani idan har tusa na hura wuta kuma kukan Kurciya jawabi ne.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel