Buhari zai mika mulkin Najeriya zuwa ga Kudu maso Yamma a 2023 - Osinbajo

Buhari zai mika mulkin Najeriya zuwa ga Kudu maso Yamma a 2023 - Osinbajo

A jiya Asabar, 22 a watan Dasumba, mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo, ya bayyana cewa, mulkin kasar nan a shekarar 2023, zai kasance a hannun yankin Kudu maso Yammacin Najeriya muddin suka marawa shugaba Buhari baya a zaben kasa na badi.

Za ku ji cewa, mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo, ya shawarci 'yan uwan sa Yarbawa akan sake zage dantsen su da daura damarar tabbatar da nasarar shugaban kasa Muhammadu Buhari a zaben 2019 domin su ci gajiyar kujerar sa a 2023.

Mataimakin shugaban kasar ya yi furucin hakan ne yayin kaddamar da yakin neman zaben jam'iyyar su ta APC na gida-gida, inda ya yi wata ganawar sirrance da Sarkin Oyo mai rike ta sarautar Alaafin Oyo, Oba Lamidi Adeyemi.

Buhari zai mika mulkin Najeriya zuwa ga Kudu maso Yammacin Najeriya a 2023 - Osinbajo

Buhari zai mika mulkin Najeriya zuwa ga Kudu maso Yammacin Najeriya a 2023 - Osinbajo
Source: Facebook

Osinbajo ya jaddada cewa, Yarbawa ke da cancantar jagorancin kasar nan a 2023 da kuma hakan ba zai tabbata ba face shugaban kasa Buhari ya yi nasara a zaben 2019.

Majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, tawagar Mataimakin shugaban kasa ta hadar da gwamna Abiola Ajimobi na jihar Oyo, dan takarar kujerar gwamna na jam'iyyar APC a jihar; Cif Bayo Adelabu da kuma saura jigan-jigan jam'iyyar APC na jihar.

KARANTA KUMA: Gwamnatin jihar Kano ta bayar da kwangilar N15.28bn ta aikin gadar sama

Osinbajo ya kara da cewa, dole al'ummar Najeriya su mike tsaye wajen tabbatar da nasarar shugaba Buhari domin ya ci gaba da fatattakar mahandama ma su ci da rashawa da yiwa tattalin arziki zagon kasa.

Jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, wata jigo ta jam'iyyar APC, Hajiya Naja'atu Muhammad, ta ce yaki da rashawa na gwamnatin shugaba Buhari da jam'iyyarsa ba wani abu bane face shafa labari shuni domin yaudarar al'ummar kasar nan.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel