Abinda yasa 'yan Najeriya ba zasu manta da Buhari ba - Fayose

Abinda yasa 'yan Najeriya ba zasu manta da Buhari ba - Fayose

Tsohon gwamnan jihar Ekiti, Mista Ayodele Fayose, ya ce 'yan Najeriya ba zasu taba mantawa da shugaba Buhari ba saboda yadda ya lalata tattalin arzikin Najeriya da kuma karfafa kabilanci a cikin tafiyar da gwamnati.

Fayose, jagoran yakin neman zaben PDP a yankin kudu maso yamma, ya ce: "bayan yakin basasa, ba a taba samun wani lokaci da aka kashe dakarun soji a Najeriya ba kamar yadda take faruwa a karkashin gwamnatin Buhari ba."

A cikin jawabin na Fayose da Lere Olayinka, mai taimaka masa a bangaren watsa labarai, ya ce, "a shekarar 2014, buhun shinkafa N7,000 amma yanzu N20,000 ne yayin da ragowar kayan masarufi suka fi karfin talaka."

A cewar Fayose, 'yan Najeriya ba zasu manta da shugaban kasar da ya samu farashin man fetur a N86.50 kowacce lita ba amma ya kara shi zuwa N145 kuma ya mayar da farashin dala zuwa N360 daga N197 bayan ya yi alkawarin cewar dala zata koma N1.

Abinda yasa 'yan Najeriya ba zasu manta da Buhari ba - Fayose

Fayose
Source: Depositphotos

"Jama'ar Najeriya ba zasu manta da shugaba Buhari ba saboda rashin girmama dokokin Najeriya da bin doka da kuma nuna son kai a yin amfani da doka ta hanyar amfani da hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) da kuma hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) a kan abokan hamayyar sa na siyasa.

DUBA WANNAN: Kisan mutane uku: Dan majalisar wakilai daga Kano ya shiga tsaka mai wuya

"Mutanen jihohin Benuwe, Filato, Taraba, Adamawa, Ekiti da ragowar wasu jihohi ba zasu manta da yadda Buhari ya bar 'yan uwansa makiyaya suka kashe masu 'yan uwa tare da lalata masu gonaki," a cewar Fayose.

Tsohon gwamnan ya ce Allah zai kwaci Najeriya daga hannun shugaba Buhari daga watan Fabrairu na shekarar 2019.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel