Zaben 2019: Oshiomhole ya yi wa Okorocha kaca-kaca

Zaben 2019: Oshiomhole ya yi wa Okorocha kaca-kaca

- Oshiomhole ya caccaki Okorocha inda ya kira shi da magoya bayan sa a matsayin batattu kuma ‘yan boge da ‘yan gangan

- Yace babu abunda ya tsinana a jiharsa na alkhairi

- Shugaban Jam’iyyar APC, Adams Oshiomhole, ya jaddada cewa Buhari na goyon bayan dan takarar gwamnan jihar Imo Sanata Hope Uzodimma dari bisa dari

Shugaban Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na Kasa, Adams Oshiomhole, ya bayyana cewa Shugaba Muhammadu Buhari na goyon bayan dan takarar gwamnan jihar Imo Sanata Hope Uzodimma dari bisa dari.

Ya bayyana haka jiya Juma’a, 21 ga watan Disamba a lokacin da jam’iyyar ta kaddamar da kamfen da dan takarar gwamna wanda Okorocha ba ya goyon baya.

Zaben 2019: Oshiomhole ya yi wa Okorocha kaca-kaca

Zaben 2019: Oshiomhole ya yi wa Okorocha kaca-kaca
Source: Facebook

A wurin kamfen, Oshiomhole ya yi wa Okorocha kaca-kaca inda ya kira shi da magoya bayan sa a matsayin batattu kuma ‘yan boge da ‘yan gangan.

Ya ci gaba da gwasale gwamnan, ya na nuna zamanin mulkin sa ba alheri ba ne a jihar Imo.

Ya kuma tunatar wa jama’a irin ragabzar da Okorocha ya rika yi a lokacin da ya ke gwamna, har ya tunatar da su wani furuci da aka yi ikirarin cewa gwamnan ne ya furta da bakin sa, inda ya ce jihar Imo ta na da kudin da za ta yi ayyuka, amma ba ta da kudin biyan ma’aikata albashi.

KU KARANTA KUMA: Wasan kwaikwayo gwamnatin Buhari ke yi da sunan yaki da rashawa – Naja’atu

Oshiomhole ya shaida wa ma’aikata cewa Uzodimma ba zai yi wasa da albashin su ba, su ma sarakunan gargajiya zai martaba su kuma ya mutunta su, ba zai yi musu rikon-sakainar-kashi ba.

Ya ce al’ummar jihar Imo sun dandana bakin mulkin Okorocha na shekaru takwas, amma idan suka zabi Uzodimma, to sannan za su gane dadin canji da kuma karsashin mulkin dimokradiyya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel