Idan ajali ya yi kira: Ma'aikacin gwamnatin tarayya ya yanke jiki ya fadi matacce

Idan ajali ya yi kira: Ma'aikacin gwamnatin tarayya ya yanke jiki ya fadi matacce

Wani ma'aikacin hukumar kula da filayen jiragen sama na kasa, FAAN, Usman Mohammed ya yanke jiki ya fadi matacce a jiya Juma'a yayin da ya ke bakin aikinsa a filin sauka da tashin jirage na Murtala Mohammed da ke Legas.

Olayinka Abioye, tsohon sakatare janar na kungiyar ma'aikatan filayen jiragen sama, NUATE, ya tabbatar wa kamfanin dillancin labarai na kasa NAN rasuwar a ranar Asabar a Legas.

Mr Abioye ya ce: "Marigayin tsohon shugaba na a NUATE, rashen FAAN.

"An ce yana bakin aikinsa ne a jiya kwatsam ya yanke jiki ya fadi matacce tun kafin a kai shi asibiti."

Idan ajali ya yi kira: Ma'aikacin gwamnatin tarayya ya yanke jiki ya fadi matacce

Idan ajali ya yi kira: Ma'aikacin gwamnatin tarayya ya yanke jiki ya fadi matacce
Source: Depositphotos

DUBA WANNAN: Gugar zana: Bayan Allah da Buhari wani kato baya bamu tsoro - Gwamnan APC

Ya ce marigayin ya rasu ya bar mata daya da yara biyar kuma tuni anyi jana'izarsa kamar yadda koyarwar addinin musulunci ya tanada.

Mr Abioye ya ce rasuwar Mohammed abin bakin ciki ne inda ya kara da cewa ya dace mahukuntan FAAN su bawa walwala da jin dadin ma'aikatansu muhimmanci.

A cewarsa, wasu daga cikin masu aikin tsaro a filin tashin jiragen suna aiki na fiye da sa'o'i takwas ba tare da hutu ba ko wani alawus na musamman.

"Wasu daga cikinsu na aiki na sa'o'i 12 a lokaci guda ba tare da hutu ba kawai saboda hukumar tana fama da tsananin karancin ma'aikata," inji shi.

Mr Abioye ya ce duk da cewa FAAN tana daukan ma'aikata daga lokaci zuwa lokaci, ba a gudanar da daukan ma'aikatan kamar yadda ya dace saboda dalilan siyasa.

Ya yi kira ga mahukunta na FAAN su samar da karin ma'aikata a filin jiragen sama da kuma asibitoci domin kare afkuwar hakan a gaba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel