2019: Osinbajo ya fadawa Yarabawa ribar da za su girba idan suka zabi Buhari

2019: Osinbajo ya fadawa Yarabawa ribar da za su girba idan suka zabi Buhari

- Mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo ya yi kira da al'ummar Yarabawa su zabi Buhari a 2019 muddin suna son mulki ya dawo hannunsu a 2023

- Osinbajo ya yi wannan kirar ne a yayin da ya kai ziyara fadar Alaafin na Oyo, Lamidi Adeyimi 111 tare da jiga-jigan jam'iyyar APC na yankin

- Mataimakin shugaban kasar ya ce idan yarabawa suka bari wannan damar ta wuce su, za a dauki lokaci mai tsawo kafin su samu shugabanci

Mataimakin shugaban kasar Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo ya ce wuka da nama yana wurin 'yan uwansa Yarabawa domin ganin cewa bayarabe dan uwansu ya maye gurbin shugaba Muhammadu Buhari a shekarar 2023 idan Buhari ya yi tazarce.

Mr Osinbajo ya yi wannan jawabin ne a ganawarsa da Alaafin na Oyo a garin Ibadan, inda ya bukaci Yarabawa sun dage domin ganin Shugaba Buhari ya yi nasara a shekarar 2019. Ya ce za a dauki lokaci mai tsawo bayarabe ya mulki Najeriya idan Buhari bai koma mulki ba a 2019.

Osinbajo ya fadawa Yarabawa yadda za su karbi mulki a 2023

Osinbajo ya fadawa Yarabawa yadda za su karbi mulki a 2023
Source: Facebook

DUBA WANNAN: Badeh ya gana da Aisha da babban hadimin Buhari kafin a kashe shi - Rahoto

A cikin jawabinsa da ya yi a fadar Alaafin, Lamidi Adeyimi 111, mataimakin shugaban kasar ya ce Shugaba Muhammadu Buhari ya taka rawar gani saboda haka ya dace a bashi damar ya zarce karo na biyu.

Wadanda suka raka Osinbajo fadan Sarkin sun hada da Gwamnan jihar Oyo, Abiola Ajimobi, dan takarar gwamna na jam'iyyar APC a jihar, Adebayo Adelabu, tsohon jagoran majalisar dattawa, Teslim Folarin da Akeem Adeyemi mai wakitan mazabar Atiba/Afijio/Oyo East/Oyo West a majalisar wakilai na taraya.

Osinbajo ya ce ya ziyarci Sarkin ne domin ya kai gaisuwa kuma ya nemi shawara daga gareshi.

"Zaben 2019 namu ne. Abinda muke kallo shine 2023 ba 2019 ba. Idan mukayi nasara a 2019, Yarabawa za su samu a 2023 amma idan bamu yi nasara a 2019 ba zai yi wahala mu samu a 2023. Ya kamata mu kalli gobe ba yau ba. Abinda mu keyi yanzu duk saboda gobe ne."

"Buhari mutum ne mai gaskiya da nagarta. Idan ya yi alkawarin zai aikata abu, toh babu shakka zai aikata abin," inji shi.

Ya yi kira da mutanen kudu maso yamma suyi watsi da jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), saboda Buhari ya fara dora Najeriya a kan turbar cigaba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel