Kiristoci 458 daga jihar Adamawa sun tafi sauke farali a Kasar Isra'ila

Kiristoci 458 daga jihar Adamawa sun tafi sauke farali a Kasar Isra'ila

A yayin da kowace shekara musulman Najeriya su kan shilla zuwa kasa mai tsarki domin sauke faralin su na aikin hajji, hakan take ga Kiristocin Najeriya da rabon su ya tsaga wajen shillawa zuwa birnin Kudus domin sauke irin na su faralin na ibadun su.

Mun samu cewa kashin farko na maniyyatan Kiristoci 458 da za su sauke farali a yau Asabar sun keta hazo daga filin jirgin saman kasa da kasa da ke birnin Yola zuwa Isra'ila.

Babban sakataren hukumar jin dadin masu sauke faralin reshen jihar Adamawa, Mista Joshua Dauda Atiku, shine ya bayyana hakan yayin ganawar sa da manema labarai a yau Asabar cikin birnin Yola.

Mista Atiku yayin zayyana tsare-tsaren hukumar dangane da maniyyatan jihar Adamawa tare haskaka jadawalin tashin jiragen su, ya ce kashi na biyu na maniyyatan za su keta hazo a ranar Laraba, 26 ga watan Dasumba.

Kiristoci 458 daga jihar Adamawa sun tafi sauke farali a Kasar Isra'ila

Kiristoci 458 daga jihar Adamawa sun tafi sauke farali a Kasar Isra'ila
Source: UGC

Ya ke cewa, babbar manufar hukumar ita ce tabbatar da jin dadin maniyyata yayin da su ke neman tabarraki da kuma tsarkake kawunan su daga zunubai domin su zamto al'umma ta gari da ko shakka ba bu hakan zai yi tasiri na samar da ci gaba a zamantakewar su, jiha da kuma kasa baki daya.

Majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, Mista ya furta hakan ne yayin taron wayar da kai da kuma fadakarwa da aka gudanar domin maniyyatan a babban cocin LCCN Cathedral da ke garin Jimeta a birnin Yola.

KARANTA KUMA: Hukumar FRSC ta yiwa Jami'ai 4,660 karin girma

Ya nemi su da su jajirce wajen aiwatar da ibadun domin samun babban rabo gami da nuna halayya ta gari a matsayin su na jakadu masu kare martabar Najeriya tare da yin kira a gare su na yiwa kasar addu'o'i managarta.

Cikin gudanar da hudubar sa, Fasto Ibrahim Audu, ya hikaito wasu ayoyi daga cikin littafin mabiya addinin Kirista dangane da yadda birnin Kudus ya kasance tsarkakakken wuri na sauke farali domin neman tabarraki da kuma tsira.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel