2019: Tsarin PDP ya fi na APC - Saraki

2019: Tsarin PDP ya fi na APC - Saraki

Shugaban majalisar dattijai, Sanata Bukola Saraki, ya bawa 'yan Najeriya tabbacin cewar zasu ga tsari mai kyau da ya fi na APC idan suka zabi jam'iyyar PDP a zaben 2019.

Saraki na wannan kalamai ne a garin Ilorin jihar Kwara yayin wata ziyarar godiya da ya kai wa magoya bayansa.

Shugaban majalisar ya jajantawa jama'ar jihar Kwara a kan yadda gwamnatin tarayya karkashin jagorancin jam'iyyar APC tayi burus da matsalolinsu duk da irin kuri'un da suka zazzaga mata a zaben shekarar 2015.

Kazalika, ya fadawa jama'ar jihar ta Kwara cewar kar gwuiwar su tayi sanyi a kan abinda jam'iyyar APC tayi masu, yana mai basu tabbacin cewar jam'iyyar PDP karkashin jagorancin Atiku Abubakar zata share masu hawaye daga shekara mai zuwa.

2019: Tsarin PDP ya fi na APC - Saraki

Saraki
Source: Depositphotos

"Yau ban zo nan don yakin neman zabe ba. Nazo ne domin yi maku godiya bisa goyon bayan da ku ke bani. Ku cigaba da bamu goyon baya da kuma goyon bayan jam'iyyar mu ta PDP da zata karbi mulki a zaben shekarar 2019.

DUBA WANNAN: Kisan mutane uku: Dan majalisar wakilai daga Kano ya shiga tsaka mai wuya

"Bamu ji dadin yadda jam'iyyar APC ta manta da ku ba duk da goyon bayan da ku ka bata a zaben shekarar 2015. Ina yi maku albishir da cewar zaku ga banbanci idan jam'iyyar PDP ta kafa gwamnati a 2019.

"Ba zamu yi maku abinda da jam'iyyar APC tayi maku ba. Zamu cika dukkan alkawuran da muka daukarwa 'yan Najeriya," a kalaman Saraki.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel