Duk da cewa an kashe Alex Badeh - EFCC zata kwace kadarorinsa

Duk da cewa an kashe Alex Badeh - EFCC zata kwace kadarorinsa

- Hukumar dake yaki da cin hanci da rashawa da kuma yiwa dukiyar al'umma zagon kasa (EFCC) zata ci gaba da bin diddigin tuhumar da take yiwa tsohon hafsan tsaro na kasar

- Wani jami'in hukumar da ya bukaci a sakaya sunansa, ya ce idan hukumar ta kammala bincike, zata kwace kadarorinsa, duk da cewar an kashe shi

- Hukumar EFCC a cikin watan Oktoba, ta kulle wannan tuhuma da take yiwa tsohon hafsan rundunar sojin saman, da take zarginsa da handame N3.9bn

Hukumar dake yaki da cin hanci da rashawa da kuma yiwa dukiyar al'umma zagon kasa (EFCC) zata ci gaba da bin diddigin tuhumar da take yiwa tsohon hafsan tsaro na kasar, Air Chief Marshal Alex Badeh, wanda kuma hakan ke nuni da cewa hukumar zata kwace kadarorinsa, duk da cewar an kashe shi.

Wani jami'in hukumar EFCC, wanda ya bukaci a sakaya sunansa, ya bayyana cewa hukumar EFCC ta yanke shawarar ci gaba da bin diddigin zargin da take yiwa marigayi Alex Badeh don cimma matsaya, tare da kwato duk wasu kayayyaki da suke mallakin marigayin.

KARANTA WANNAN: Ra'ayin Farfesa Hezekiah: APC bata da wani dalili na sake tsayar da Buhari a 2019

Duk da cewa an kashe Alex Badeh - EFCC zata kwace kadarorinsa

Duk da cewa an kashe Alex Badeh - EFCC zata kwace kadarorinsa
Source: UGC

Idan za a iya tunawa, kafin a kashe shi, Badeh na fuskantar tuhuma tare da kamfanin Iyalikam Nigeria Ltd, a gaban mai shari'a Okon Abang na babbar kotun tarayya da ke Maitama, Abuja, wanda ake zarginsa da yin amfani da ofishinsa wajen karkatar da kudaden rundunar sojin sama ta Nigeria (NAF), wanda ya sayi kadarori don amfanin kansa a Abuja.

Hukumar EFCC a cikin watan Oktoba, ta kulle wannan tuhuma da take yiwa tsohon hafsan rundunar sojin saman, da take zarginsa da handame N3.9bn.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel