Yunkurin kawo karshen Saraki: Yan jam'iyyar PDP 5000 sun koma APC a jihar Kwara

Yunkurin kawo karshen Saraki: Yan jam'iyyar PDP 5000 sun koma APC a jihar Kwara

- Mutan jihar Kwara sun ce lokaci ya zo na soke sarautar Saraki a jihar

- Bayan nasarar da APC a samu a jihar kwanakin, ta sake samun karuwa

Akalla mutane 5,000 daga sassa daban-daban na mazabar Kwara maso kudu a ranan Asabar sun sauya sheka daga jam'iyyar Peoples Democratic Party PDP zuwa All Progressives Congress (APC) a wani taron siyasa a garin Omu-Aran, jihar Kwara.

Wadanda suka sauya shekan sun samu kyakkyawan tarba a taron kaddamar yakin neman zaben mazabar Ekiti/Irepodun/Isin/Oke-Ero na jihar kuma an basu katin zaman yan jam'iyyar.

Shugabannin wadanda suka sauya a jawabansu sun bayyana jin dadinsu da shirin bada nasu gudunmuwar wajen tabbatar da cewa jam'iyyar ta samu nasara a zaben 2019.

Game da cewarsu, jam'iyyar APC ce kadai za ta iya taimakawa wajen cigaban jihar da kas aga baki daya. Baban jigon jam'iyyar PDP, Dakta Seyi Adigun, ya ce duk wani dan siyasa mai hankali ya san irin shawarar da ya kamata yayiwa rana gobensa.

Adigun, wanda babban jami'in ma'aikatar ilimi a jihar ne ya bayyana cewa yana wakiltan akalla mutane 1500 ne kuma sun amince cewa jam'iyyar APC ce mai niyyar taimakon Najeriya da yan Najeriya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel