Ra'ayin Farfesa Hezekiah: APC bata da wani dalili na sake tsayar da Buhari a 2019

Ra'ayin Farfesa Hezekiah: APC bata da wani dalili na sake tsayar da Buhari a 2019

- Farfesa Daddy Hezekiah, ya ce jam'iyyar APC bata da wasu kwararan dalilai na sake gabatar da Muhammadu Buhari a matsayin dan takararta na shugaban kasa a zaben 2019

- Hezekiah ya ce tun bayan da Buhari ya shiga ofis har zuwa yanzu, babu wani abun azo a gani da yayi kan farfado da tattalin arziki da kuma gine ginen kasar

- Ya ce a karkashin mulkin Buhari, talauci, rashin aikinyi da kuma kashe kashe sun karu. Ga kuma tabarbarewar kayan more rayuwa musamman ma rashin tituna

Shugaban jami'ar Hezekiah, da ke Umudi, jihar Imo, kuma wanda ya samar da majami'ar Living Christ Mission, Farfesa Daddy Hezekiah, ya ce jam'iyyar APC bata da wasu kwararan dalilai na sake gabatar da Muhammadu Buhari a matsayin dan takararta na shugaban kasa a zaben 2019.

Farfesa Hezekiah wanda ya zanta da manema labarai, ya bayyana cewa shugaban kasa Muhammad Buhari ya ci amanar 'yan Nigeria.

Hezekiah ya ce tun bayan da Buhari ya shiga ofis har zuwa yanzu, babu wani abun azo a gani da yayi kan farfado da tattalin arziki da kuma gine ginen kasar, wanda a cewarsa, bai cancanci ya sake zama shugaban kasar ba.

KARANTA WANNAN: Tsuntsun da ya ja ruwa: Wasu 'yan Yahoo Yahoo guda 2 sun gamu da fushin kotu

Ra'ayin Farfesa Hezekiah: APC bata da wani dalili na sake tsayar da Buhari a 2019

Shugaban kasa Muhammadu Buhari
Source: Facebook

Farfesan ya ce: "Maganar gaskiya, har yanzu na kasa gane dalilin da ya sa APC ta sake tsayar da Buhari. Ni bana tare da kowanne dan takara ko jam'iyya, sai dai ina ganin tabbas APC ta yi babban kuskure na sake tsayar da Buhari, domin kamata yayi ace ta dauko wani mutum daban."

"A karkashin mulkin Buhari, talauci, rashin aikinyi da kuma kashe kashe sun karu. Tabarbarewar kayan more rayuwa musamman ma rashin tituna. Idan har zai bukaci sake tsayawa takara, to ya gabatarwa jama'a ayyukan da gwamnatinsa a yanzu ta yi."

Hezekia ya ce ya zama wajibi 'yan Nigeria su kasa, su tsare, su raka, kuma a kirga kuri'unsu a gabansu, yana mai cewa tsarin A4 shine mafi dacewa da tsarin zaben kasar Nigeria.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel