Hukumar FRSC ta yiwa Jami'ai 4,660 karin girma

Hukumar FRSC ta yiwa Jami'ai 4,660 karin girma

- Hukumar FRSC ta yiwa jami'an ta manya da kanana karin girma a fadin Najeriya

- Hukumar ta gargadi jami'anta kan tsayuwara daka tare da jajicewa bisa aiki tukuru

- Shugaban hukumar FRSC na kasa ya sha alwashin ci gaba da inganta jin dadin jami'an sa

Hukumar kiyaye aukuwar hadurra ta Najeriya, FRSC, ta yi jami'anta 4,660 karin girma a fadin Najeriya biyo bayan amincewar sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito.

Jami'in hulda da al'umma na hukumar, Mista Bisi Kazeem, shine ya bayar da labarin wannan lamari cikin wata sanarwa da amincewar shugabancin hukumar.

Cikin wadanda suka samu karin girma da kuma matsayi sun hadar da manyan jami'ai 1,310, yayin da kananan jami'ai 3,350 suka samu na su babban rabon.

Hukumar FRSC ta yiwa Jami'ai 4,660 karin girma

Hukumar FRSC ta yiwa Jami'ai 4,660 karin girma
Source: Depositphotos

A yayin da hukumar da fantsama cikin shirye-shirye na tabbatar da wannan karin matsayi ga jami'anta, majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, karin girman zai fara tasiri ne tun daga ranar 27 ga watan Nuwamba da ya gabata.

Mista Kazeem ya isar da sakon shugaban hukumar na kasa, Mista Boboye Oyeyemi, na taya murna ga jami'an da suka samu kyautatuwar hukumar a halin yanzu.

Ya gargade su kan tsayuwa tare da jajircewa bisa aiwatar da ayyukan su cikin kwazo domin cimma manufa da suka sanya a gaba.

KARANTA KUMA: Boko Haram: Dakarun Soji sun nemi a daina tura su aiki Arewa maso Gabashin Najeriya

Oyeyemi ya kuma bayar da tabbacin cewa, hukumar za ta kara kaimi wajen inganta jin dadin jami'anta domin ramawa Kura kyakkyawar aniyyarta.

Kazalika jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, a yau Asabar, shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya jagorancin taron kungiyar shugabannin kasashen Afirka ta Yamma a babban birnin kasar nan na tarayya.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel