Yajin aiki: Ana gab da zabe, kungiyar kwadago za ta gudanar da zanga-zanga kare dangi

Yajin aiki: Ana gab da zabe, kungiyar kwadago za ta gudanar da zanga-zanga kare dangi

Kungiyar kwadagon Najeriya watoo NLC ta alanta ranar 8 ga wa tan Junairu a matsayin ranar gudanar da zanga-zangan kare dangi kan mafi karancin kudin albashin ma'aikatan Najeriya da yaki ci, yaki cinyewa.

An yanke wannan shawara ne a ganawar shugabannin kungiyar NLC a Abuja inda shugaban kungiyar ya kwadagon , Ayuba Wabba, ya saki jawabi.

Hukumar NLC na bukatan gwamnatin tarayya ta kara mafi karancin kudin albashin ma'aikata daga N18,000 zuwa N30,000 kuma gwamnatocin jihohi sun amince zasu biya amma suna jinkiri.

Yayin gabatar da kasafin kudin 2019, shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa za'a kafa kwamitin tattaunawa kan bukatar NLC amma gwamnoni sun ce N22,500 zasu iya biya.

Shugaban hukumar ya yi Allah wadai da jinkirin da gwamnatin tarayya keyi wajen gabatar da dokar mafi karancin kudin albashin gaban majalisar dokokin tarayya domin tabbatarwa.

KU KARANTA; APC bata da wani dalili na sake tsayar da Buhari a 2019

A baya mun kawo muku rahoton cewa Kungiyar Gwamnonin Najeriya (NGF) ta bayyana cewar ba ta adawa ta yiwa ma'aikata karin mafi karancin albashi da Kungiyar Kwadago na kasa ke nema.

Ciyaman din kungiyar, Gwamna Abdulaziz Yari na jihar Zamfara ne ya bayyana wa manema labarai hakan a jiya Laraba bayan kungiyar tayi taro a Abuja.

Ya ce matsalar ba wai adadin mafi karancin albashin da gwamnonin za su iya biya bane amma samuwar kudaden da gwamnonin za suyi amfani dashi domin biyan albashin da kungiyar kwadago (NLC) ke bukata.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel