Kudin da muke rabo na bashi da wata alaka da neman tazarce - Farfesa Qanen shugaba Buhari

Kudin da muke rabo na bashi da wata alaka da neman tazarce - Farfesa Qanen shugaba Buhari

- Shirin trademoni anyi shi ne don tallafawa yan kasuwa

- Abin tsoratarwa ne da wasu suke cewa don kuri'u APC ta fito da shirin

- Majalisar dattawa ce ta amince da tallafin ga yan kasuwa

Kudin da muke rabo na bashi da wata alaka da neman tazarce - Farfesa Qanen shugaba Buhari

Kudin da muke rabo na bashi da wata alaka da neman tazarce - Farfesa Qanen shugaba Buhari
Source: Depositphotos

Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya jaddada cewa shirin trademoni, shirin tallafi ga yan kasuwa na Gwamnatin tarayya ba anyi shi ne don siye kuri'un yan kasuwa ba daga jam'iyyar APC a zaben 2019 mai zuwa.

Farfesa Yemi Osinbajo ya sanar da hakan ne a yayin amsa tambayoyi daga manema labarai a filin jirgin Asaba, a hanyar shi ta komawa Abuja daga ziyarar da ya kai Warri, Ughelli da Asaba.

DUBA WANNAN: Amurka zata janye daga Afghanistan, bayan sulhu da Taliban da ta yaka tun 2001

Yace abin damuwa ne da wasu mutane ke tunanin shirin trademoni da market money wanda akayi don karfafa yan kasuwa daga gwamnatin tarayya ake zargin don kuri'u ne.

Mataimakin shugaban kasar yace majalisar dattawa ce ta amince da kudin tallafin wanda suka ce don maza da mata ne yan kasuwa don bunkasa kasuwancin su.

"Majalisar dattawa ce ta amince da shirin. Idan basa son tallafin saboda suna da wata manufa, toh abin a duba ne," inji shi

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel