Ministan tsaro ya amayar da ta cikinsa kan kashe kashen rayuka a Zamfara da Kaduna

Ministan tsaro ya amayar da ta cikinsa kan kashe kashen rayuka a Zamfara da Kaduna

- Ministan tsaro, Mansur Muhammad Dan-Ali, ya jajantawa gwamnati da kuma al'umar jihohin Zamfara da Kaduna, bisa kashe kashen rayuka a jihohin

- Ministan yi nuni da cewa ma'aikatar tsaro tare da hadin guiwar rundunar sojin Nigeria na ci gaba da bin hanyoyi don kawo karshen ta'addanci akasar

- Ya ce jami'an tsaro na aiki tukuru don kare rayuka da dukiyoyin 'yan Nigeria da kuma kare kasar daga 'yan ta'addan cikin kasar dama masu yunkurin kutsowa ciki.

Ma'aikatar tsaro ta mayar da martani kan hare haren da aka kai a jihohin Zafara da Kadunana baya bayan nan, wanda yayi silar mutuwar mutane da dama, tare da janyo asarar dokiyoyi.

Ma'aikatar, karkshin jagorancin Mansur Muhammad Dan-Ali, a yayi da take jajantawa gwamnati da kuma al'ummar jihohin Zamfara da Kaduna, ta bayyana hare haren a matsayin wani iftila'i mai tsuma zuciya.

Ministan, a yayin da yake addu'ar Allah ya gafartawa wadanda suka mutu, tare da baiwa iyalansu hakurin jure rashin da suka yi, ya yi nuni da cewa ma'aikatar tsaro tare da hadin guiwar rundunar sojin Nigeria na ci gaba da bin hanyoyi don kawo karshen ta'addanci akasar.

KARANTA WANNAN: Disamba 22: Buhari ya jagoranci taron kungiyar ECOWAS a Abuja

Ministan tsaro ya amayar da ta cikinsa kan kashe kashen rayuka a Zamfara da Kaduna

Ministan tsaro ya amayar da ta cikinsa kan kashe kashen rayuka a Zamfara da Kaduna
Source: Facebook

Kanal Tukur Gusau, jami'in hulda da jama'a na ministan taron, a cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a Abuja, a ranar Juma'a, ya ce jami'an tsaro na aiki tukuru don kare rayuka da dukiyoyin 'yan Nigeria da kuma kare kasar daga 'yan ta'addan cikin kasar dama masu yunkurin kutsowa ciki.

Sanarwar tace: "Hakika zai zama abu mai amfani idan kuka san cewa gwamnatin tarayya ta yi yunkurin samar da rundunar soi ta 8, a jihar Sokoto don kawo akrshen ta'addanci a shiyyar Arewa maso Yamma., Haka zalika, an samar da rundunar kawo daukin gagawa ta rundunar sojin sama don tallafawa dakarun daga ta sama.

"A baya bayan nan, ma'aikatar tsaro ta umurci kwamandan rundunar soji ta 8 da ya tatara komai nasa tare da dakarunsadaga Sokoto zuwa Gusau, don taimakawa aikin rundunar da ke gudanar da shirin atisayen Sharan Daji, har sai zaman lafiya ya wanzu a jihar."

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel