Boko Haram: Dakarun Soji sun nemi a daina tura su aiki Arewa maso Gabashin Najeriya

Boko Haram: Dakarun Soji sun nemi a daina tura su aiki Arewa maso Gabashin Najeriya

Sabanin rahotanni na gwamnatin tarayyar Najeriya na dukurkusar da kungiyar ta'addanci ta Boko Haram, a halin yanzu hare-haren kungiyar da ke faman aukuwa a yankunan Arewa maso gabashin kasar nan sun kai intaha.

Binciken manema labarai na jaridar The Punch ya tabbatar da cewa, wasu daga cikin dakarun sojin Najeriya, sun fara tuntube-tuntube na neman tserewa daga tafiya aiki zuwa yankunan Arewa maso Gabas sakamakon ta'addancin Boko Haram da ya ke ci gaba da ta'azzara.

Kamar yadda wasu dakarun sojin kasar nan suka shaidawa manema labarai, haren-haren kungiyar ta'adda ta Boko Haram da suka auku a kwana-kwanan nan musamman na Metele, Kangarwa, Malumfatori da kuma Arge a jihar Borno, sun firgita su kwarai da aniyya.

Boko Haram: Dakarun Soji sun nemi a daina tura su aiki Arewa maso Gabashin Najeriya

Boko Haram: Dakarun Soji sun nemi a daina tura su aiki Arewa maso Gabashin Najeriya
Source: Depositphotos

Kazalika harin yankin Buni Gari na jihar Yobe da ya auku a watan Nuwamba, ya jefa shakku cikin zukatan dakaru da a halin yanzu su ke faman neman tsira ta kauracewa yiwa Najeriya bauta a yankunan Arewa maso Gabashin kasar nan.

Majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, mafi akasarin dakarun sojin Najeriya da ke ci gaba da yiwa kasar su bauta a yankunan Arewa maso Gabashin Najeriya, na tuntube-tuntube na neman sauyin wurin aiki sakamakon fargaba ta mummunar ta'adar da ka iya aukuwa a ko da yaushe.

KARANTA KUMA: Kujerar Shugaban Kasa: Ba ni da wani shamaki da takara a zaben 2023 - Okorocha

Wani Birgediya Janar da ya bukaci a sakaya sunan sa ya bayyana cewa, da yawan dakarun soji na ci gaba da fafutikar kauracewa afkawa cikin sahun wadanda za a tura su hidima a Arewa maso Gabashin Najeriya.

Cikin wani rahoton mai nasaba da wannan, Jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, dakarun sojin kasa na Najeriya, sun samu nasarar dakile wani mummunan harin 'yan bindiga a jihar Benuwe.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel