Disamba 22: Buhari ya jagoranci taron kungiyar ECOWAS a Abuja

Disamba 22: Buhari ya jagoranci taron kungiyar ECOWAS a Abuja

A yau Asabar, 22 ga watan Disamba 2018, Shugaban kasa Muhamamdu Buhari ya jagoranci taron shuwagabannin kasashen Yammacin Afrika ECOWAS, a babban birnin tarayya Abuja.A yayin taron, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gabatar da jawabi mai dan tsayi.

Sai dai Legit.ng Hausa, ta tsamo maku wasu muhimman abubuwa 5 da shugaban kasar ya fada a yayin taron.

1. A dai dai wannan gabar, ina so na jinjinawa Nana Akuffo-Addo, shugaban kasar Ghana tare da Alpha Conde, shugaban kasar Guinea, da sauran shuwagabannin ECOWAS na kawo karshen rikicin siyasar kasar Togo. Da kuma kokarinmu gaba daya na warware rikicin siyasar Guinea Bissau. Hakika munyi namijin kokarin wajen taimakawa gwamnatin Mali da Togo wajen magance rikicin siyasar da suke fama da shi.

2. Duk da irin tarin nasarorin da aka samu, har yanzu kasashen ECOWAS na fuskantar matsaloli da dama, kama daga tattalin arziki, zaman lafiya, tsaro, shugabanci da kuma fannin kaiwa jama'a dauki. Sanin kanku ne cewa, an kafa ECOWAS don karfafa zumuncin da ke tsakanin kasashen Yammacin Afrika, da nufin bunkasa rayuwar jama'a tare da hada karfi da karfe wajen ganin ci gaban Afrika baki daya.

KARANTA WANNAN: Ya zama wajibi a kori Ramos, Modric, Mercelo idan ana so na dawo Madrid - Mourinho

Disamba 22: Buhari ya jagoranci taron kungiyar ECOWAS a Abuja

Disamba 22: Buhari ya jagoranci taron kungiyar ECOWAS a Abuja
Source: Facebook

3. Hakika abun damuwane matuka yadda ta'addanci da tashe tashen hankula ke ci gaba da barazana ga zaman lafiya da tsaro a kasashen Yammacin Afrika. Wannan kuwa na bukatar hadin karfi da karfe don kawo karshensa. A yayin da muka duka tukuru don bullo da sabbin hanyoyin kawar da ta'addanci, muna bukatar taimako daga takwarorinmu don cimma wannan manufa.

4. Har ila yau akan zaman lafiyar kasashen Yammacin Afrika, kamar yadda kowa ya sani, Nigeria da Senagal zasu gudanar da zabukansu a watan Fabreru 2019. A namu bangaren, ni tuni na sha alwashin gudanar da sahihin zabe wanda babu aringizo ko magudi a ciki. A dalilin hakan, hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC, hukumomin tsaro, da sauran masu ruwa da tsaki a harkar siyasa, sun bayyana kudurinsu na ganin an gudanar da sahihin zabe cikin lumana don gujewa tashin hankula, domin ci gaban kasar baki daya.

5. A wannan yanayi da muke ci na rashin tabbas kan tattalin arzikinmu wanda kuma kusan shine ke haddasa tashin farashin kayan masarufinmu, rudani a demokaradiyyarmu, sanna ga uwa uba gurbacewar yanayi wanda ya shafi aikin nomanmu, karuwar ta'addanci a kasashenmu, wanda kullum ke cin karensa ba babbaka, hakika dole mu hada karfi da karfe don yakar wadannan matsaloli, tare da samar da kyakkyawan muhallin rayuwa ga al'ummarmu.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel