Kujerar Shugaban Kasa: Ba ni da wani shamaki da takara a zaben 2023 - Okorocha

Kujerar Shugaban Kasa: Ba ni da wani shamaki da takara a zaben 2023 - Okorocha

- Gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha, ya ce ba bu wanda zai hana shi takarar kujerar shugaban kasa a zaben 2023

- Na fi dukkanin 'yan kabilar Ibo cancantar kujerar shugaban kasa a zaben 2023 inji gwamnan jihar Imo

- Gwamnan Rochas ya ba bu abinda yake hankoro face kasancewa shugaban kasa dan kabilar Ibo na farko cikin farar hula a Najeriya

Hakika kowa da bazarsa ya kan taka rawa daidai da irin kidin da ya karbe shi, hakan ya sanya a halin yanzu, gwamnan jihar Imo Rochas Okorocha, ya zayyana kudirin cewa ba bu abinda ya ke hankoro face kujerar shugaban kasa a zaben 2023.

Kamar yadda majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito, gwamna Rochas ya ce ba bu wani tunani da dabaibaye zuciyar sa a halin yanzu face kasancewa shugaban kasar Najeriya na farko a zaben 2023 dan kabilar Ibo karkashin mulkin farar hula na Dimokuradiyya.

Kujerar Shugaban Kasa: Ba ni da wani shamaki da takara a zaben 2023 - Okorocha

Kujerar Shugaban Kasa: Ba ni da wani shamaki da takara a zaben 2023 - Okorocha
Source: Getty Images

Rochas ya yi furucin hakan ne yayin karbar bakuncin kungiyar 'yan jarida ta Orlu Zone Congress of Journalist (OZCOJ) a fadar gwamnatin sa da ke babban birni na Owerri.

Ya ce dukkanin masu da'awar batanci a gare sa ya bayu ne a sakamakaon adawarsu dangane da kasancewar sa dan kabilar Ibo mafi cancantar kujerar shugaban kasa mai zuciyar da ta tsarkaka daga kabilanci.

KARANTA KUMA: Masifu kashi 42 sun auku cikin jihohi 3 a Kudancin Najeriya

Gwamnan ya siffanta kansa a matsayin madubin dubawa ga dukkanin 'yan kabilar Ibo da zai tabbatar da hadin kai tgami da fahimtar juna da kuma tarayya ta tabbatar da jagorancin kasar nan a hannun kabilar a shekarar 2023.

Jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, zanga-zangar cire tallafin man fetur da Biredi ta yi sanadiyar salwantar rayukan Mutane 9 a kasar Sudan.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel