Badeh ya gana da Aisha da babban hadimin Buhari kafin a kashe shi - Rahoto

Badeh ya gana da Aisha da babban hadimin Buhari kafin a kashe shi - Rahoto

- An gano cewar ashe marigayi Alex Badeh ya gana da Aisha Buhari da Abba Kyari makonni uku kafin a kashe shi

- Wani na kusa da marigayin ya ce Alex Badeh ya tafi wajen Aisha Buhari ne domin neman taimako a kan shari'ar zargin rashawa da ake masa

- Sai dai an ce Aisha Buhari ta ce shugaban ma'aikatan Buhari, Abba Kyari ne zai iya taimaka masa amma ko da suka hadu bai masa wani alkawari ba

Bincike ya nuna cewa tsohon babban hafson tsaron Najeriya, Air Cif Alex Badeh ya gana da uwargidan shugaban kasa, Aisha Muhammadu Buhari da shugaban ma'aikatan shugaba Buhari, Abba Kyari a kan shari'a tuhumarsa da rashawa da akeyi makonni uku kafin kissar gillar da wasu 'yan bindiga su kayi masa a tittin Abuja zuwa Keffi.

Badeh ya gana da Aisha da babban hadimin Buhari kafin a kashe shi - Rahoto

Badeh ya gana da Aisha da babban hadimin Buhari kafin a kashe shi - Rahoto
Source: Facebook

DUBA WANNAN: Gwamnatin tarayya ta fadi abinda ke janyo hare-haren ta'addanci a Zamfara da Kaduna

Saturday Punch ta gano cewa Badeh da ake zargi da cin amana, damfara da karkatar da kudaden gwamnati ya gana da Aisha Buhari domin neman alfarma game da shari'arsa da aka ce ya jefa shi cikin tsananin damuwa.

Wani na kusa da marigayin ya yi ikirarin cewa Badeh ya fada masa cewa Aisha Buhari ta ce Abba Kyari ne kadai zai iya taimaka masa.

"Badeh ya ce Aisha Buhari ta kai shi wajen Kyari amma bai masa wani alkawari ba. Kyarin ya ce tsohon babban hafson tsaron ya kira shi a wayan tarho amma bai same shi a wayan ba tun rannar da suka gana kimanin makonni uku da suka wuce," inji majiyar

A halin yanzu, alamu na nuna cewa hukumar yaki da masu yiwa arzikin kasa ta'annati EFCC ba za su dakatar da shari'ar da ake yiwa Badeh ba duk da cewa ya rasu.

Wani jami'in hukumar EFCC da ya ce kar a bayyana sunansa ya ce hukumar za ta cigaba da shari'ar da akeyi a kan tsohon babban hafson tsaron har sai an kwato dukkan kadarorin da ya mallaka da kudaden haramun.

Anyi kokarin ji ta bakin mai magana da yawun hukumar EFCC, Tony Orilade domin jin ta bakinsa a kan lamarin sai dai ba same shi ba har zuwa lokacin rubuta wannan rahoton a ranar Juma'a.

Shima mai taimakawa shugaban kasa na musamman a fannin kafafen yada labarai, Garba Shehu bai amsa sakon da aka aike masa ba domin jin abinda zai ce game a lamarin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel