Rikicin APC: Buhari na bukatar dakarun siyasa masu gaskiya - Oshiomhole

Rikicin APC: Buhari na bukatar dakarun siyasa masu gaskiya - Oshiomhole

- Ciyaman din jam'iyyar APC na kasa, Adams Oshiomhole ya ce shugaba Buhari yana bukatar dakarun siyasa masu gaskiya tare da shi

- Oshiomhole ya ce samun dakaru na gari ne zai bawa Shugaba Muhammadu damar cigaba da gudanar da ayyukan alkhairin da ya fara ba tare da masu zagon kasa ba

- Gwamnan jihar Umaru Tanko Al-Makura ya ce shi ya 'yan jiharsa suna goyon bayan Buhari dari bisa dari kuma sunyi na'am da salon jagorancin Oshiomhole

Shugaban jam'iyyar APC na kasa, Kwamared Adams Oshiomhole ya ce shugaba Muhammadu Buhari yana bukatar zababun mukarrabai na gari domin ya cigaba da ayyukan cigaba da alkhairi da ya fara a kasar.

Oshiomhole ya yi wannan jawabin ne a jiya, Juma'a a garin Lafia ta Jihar Nasarawa yayin da ya ke mika tuta ga dan takarar gwamna na jam'iyyar, Injiniya, Audu Sule da mataimakinsa, Dr Emmanuel Agabe.

DUBA WANNAN: Amaryar sanata Yarima da ya aura tana karama ta girma, hoto

Rikicin APC: Buhari na bukatar dakarun siyasa masu gaskiya - Oshiomhole

Rikicin APC: Buhari na bukatar dakarun siyasa masu gaskiya - Oshiomhole
Source: UGC

"Shugaba Muhammadu Buhari yana gyara kimar Najeriya a idon kasashen duniya saboda yaki da rashawa da ya fara cikin shekaru uku sakamakon barnar da jam'iyyar PDP suka kwashe shekaru 16 suna tafkawa," inji shi.

A cewarsa, kasashen duniya suna yabawa canjin da shugaba Muhammadu Buhari ya kawo wadda ke dawo da kima da kuma darajar Najeriya a idanun kasashen duniya.

A jawabinsa. tsohon gwamnan jihar Nasarwa, Sanata Abdullahi Adamu ya ce shugaba Muhammadu Buhari yana bukatar goyon bayan masu kada kuri'a ta hanyar zabar APC a dukkan zabuka domin ya samu ikon kawo cigaba a kasar ba tare da masu zagon kasa ba.

Gwamna Umaru Tanko Al-Makura na jihar ya ce 'yan jam'iyyar APC na jiharsa dukkansu kan hade yake waje guda kuma suna goyon bayan Shugaba Muhammadu Buhari kuma sunyi na'am da irin salon jagorancin Oshiomhole.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel