Na shirya yadda zan samu biliyoyi daga garkuwa da mutane - Wanda ake zargi

Na shirya yadda zan samu biliyoyi daga garkuwa da mutane - Wanda ake zargi

- Rundunar 'yan sanda a jihar Niger ta cafke wani mai garkuwa da mutane, wanda ake zargin ya kitsa tuggun sace wani mutumi mai suna Abubakar Umar

- A jawabin fallasa kansa da ya rubuta, wanda ake zargin mai shekaru 24, Mukhtar Abubakar, ya ce ya kammala shirin samun biliyoyi ta hanyar garkuwa da mutane

- Mukhtar ya bayyana cewa garkuwa da mutane yanzu ta zama hanya mafi sauki ta samun kudi a Nigeria

Rundunar 'yan sanda ta jihar Niger ta cafke wani mamban kungiyar masu garkuwa da mutane, wanda ake zargin ya kitsa tuggun sace wani mutumi mai suna Abubakar Umar na garin Auna, a karamar hukumar Magama da ke cikin jihar.

A jawabin fallasa kansa da ya rubuta, kuma ya zanta da jaridar The Nation, wanda ake zargin mai shekaru 24, Mukhtar Abubakar, ya ce ya kammala shirin samun biliyoyi ta hanyar garkuwa da mutane, sai dai cafke shi da akayi ya rushe wannan shirin, yana mai cewa garkuwa da mutane yanzu ta zama hanya mafi sauki ta samun kudi a Nigeria.

Ya bayyana cewa yunkurinsu a kullum shine su sace mutum, su bukaci kudin fansa daga iyalansa kafin su sake shi. Ya ce garkuwa da mutane a cikin shekarun baya ya sama masa makudan kudade.

KARANTA WANNAN: Babbar magana: PDP ta kalubalanci Buhari akan zargin boye N2.6tn na harajin man fetur

Na shirya yadda zan samu biliyoyi daga garkuwa da mutane - Wanda ake zargi

Na shirya yadda zan samu biliyoyi daga garkuwa da mutane - Wanda ake zargi
Source: Facebook

"Garkuwa da mutane itace hanya mafi sauki ta samun kudi a Nigeria; zaka iya samun biliyoyi ba tare da ka sha wata wahala ba. Ina kaunar sace mutane, saboda samun kudin fansa kafin na sake su."

Sai dai, dubun Mukhtar ta cika ne a lokacin da suka bukaci kudin fansar Umar.

A cewar Mukhtar, da shi da tawagarsa sun shiga gidan Umar, inda suka sace shi tare da bukatar N150m daga iyalansa a matsayin kudin fansa, wanda har aka yanke matsayar biyan 13.5m domin sakinsa.

Mukhtar ya bayyana cewa tawagar tas ta mutane tara ce, inda suke da jagora Mallam Umaru. Sai dai ya ce shi dubunsa ta cika okacin da rundunar yan sanda suka cafke shi a Kontagora a lokacin da yake kokarin tserewa, sai dai akwai sauran abokan aikinsa da dama.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Tags:
Mailfire view pixel