Gwamnatin tarayya ta fadi abinda ke janyo hare-haren ta'addanci a Zamfara da Kaduna

Gwamnatin tarayya ta fadi abinda ke janyo hare-haren ta'addanci a Zamfara da Kaduna

- Gwamnatin tarayya ta ce shaye-shayen miyagun kwayoyi da rashin ayyukan yi suna daga cikin abubuwan da ke kara janyowar tabarbarewa tsaro a Zamfara da Kaduna

- Wannan sanarwar ta fito ne daga bakin Ministan Tsaro, Mansur Dan-Ali a tsokacin da ya yi game da sabuwar harin da 'yan bindiga suka kai a Zamfara

- Ministan ya ce gwamnati za ta cigaba da kara mayar da hankali wajen magance matsalar kuma ya nemi hadin kan dukkan masu ruwa da tsaki a fannin tsaro

A jiya, Alhamis 20 ga watan Disambar 2018 ne gwamnatin tarayya ta bakin Ministan Tsaro, Mansur Dan-Ali ta sake jadada cewa shaye-shayen migayun kwayoyi da matasa keyi ne dalilin da yasa ake samun yawan hare-hare a jihohin Zamfara da Kaduna.

Ministan ya yi wannan jawabin ne yayin da ya ke tsokaci a kan sabuwar harin da 'yan bindiga suka kai a Zamfara cikin kwanan nan.

Gwamnati ta fadi abubuwan da ke janyo hare-hare a Zamfara da Kaduna

Gwamnati ta fadi abubuwan da ke janyo hare-hare a Zamfara da Kaduna
Source: Facebook

DUBA WANNAN: Amaryar sanata Yarima da ya aura tana karama ta girma, hoto

Gwamnatin tayi kira ga masu ruwa da tsaki su bayar da gudunmawa domin magance kallubalen inda ta ce cikin shekaru uku da suka gabata, gwamnatin tarayya da hukumar sojin Najeriya sun mayar da hankali a kan yaki da 'yan ta'ada musamman a yankin Arewa maso yamma na kasar.

A wata sanarwa mai dauke da sa hannun mai magana da yawun ministan, Colnel Tukur Gusau, Ministan tsaro, Mansur Mohammed Dan Ali ya ce Ma'aikatan Tsaro da bayar da umurnin kafa sabuwar rundunar soji ta musamman domin magance kallubalen 'yan bindiga a yankin.

Ga wani bangare daga cikin sakon Ministan: "A cikin 'yan kwanakin nan, ma'aikatan tsaro ta umurci GOC 8 ta mayar da headkwatan dabarun yaki daga Sokoto zuwa Gusau domin taimakawa atisayen Sharan Daji har sai an samu zaman lafiya a jihar.

"An dauki wannan matakan ne domin cimma burin gwamnatin tarayya na tabbatar da tsaron lafiya da kiyaye dukiyoyin al'umma.

"Sai dai abin lura ne yadda matsalar shaye-shayen miyagun kwayoyi, rashin ayyukan yi da sauransu ke bayar da gudunmawa wajen tabarbarewar harkar tsaro a jihar Zamfara.

"Haka yasa ake kira ga dukkan masu ruwa da tsaki da su hada karfi da karfe waje guda domin taimakawa hukumomin tsaro wajen ganin an magance matsalar tsaron."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel